Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, ya isa Filin Jirgin Sama na Sam Mbakwe International Cargo da ke Owerri, Jihar Imo a ranar Juma’a domin kaddamar da jirgin farko na alhazai daga Najeriya zuwa Saudiyya domin aikin Hajjin 2025.
KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN: Ana sa ran mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa Aikin Hajjin Bana
A lokacin da ya sauka a filin jirgin, Gwamna Hope Uzodinma na Jihar Imo, Shugaban Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, da wasu manyan jami’an gwamnati ne suka tarbe shi.
Wannan bikin ya zama tarihi domin yana nuna fara tashi na farko na jirgin kasa da kasa daga filin jirgin saman Imo, inda akalla alhazai 315 daga jihohin Imo, Abia da Bayelsa suka hau jirgin kamfanin Air Peace zuwa Saudiyya.
A bana, ana sa ran alhazai sama da 43,000 daga jihohi 36 na Najeriya da Babban Birnin Tarayya (FCT) za su halarci aikin hajji tare da sauran musulmi daga sassa daban-daban na duniya.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, ya bayyana cewa hukumar na da cikakken shiri domin gudanar da hajjin bana cikin nasara.
Ya kuma bukaci hadin kai da jajircewar dukkan masu ruwa da tsaki domin samar da ingantaccen hidima ga alhazai.
“Na tabbatar wa dukkanin masu ruwa da tsaki cewa NAHCON za ta ci gaba da hada kai da kowa tare da karfafa gwiwa domin ganin an samu nasarar Hajjin 2025,” in ji shi.
Shi ma da yake nasa jawabin, Kwamishinan Ayyuka na NAHCON, Alhaji Anofi Elegushi, ya tabbatar da kudurin hukumar na ci gaba da inganta ayyukanta da walwalar alhazai.
NAN