Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da samun nasarar jigilar maniyyata zuwa garin Mina na kasar Saudiyya, a daidai lokacin da aka fara gudanar da aikin Hajjin.
Ibrahim Garba Shuaibu, Shugaban tawagar ‘yan jaridu na Jihar Kano, wanda kuma ya kasance Sakataren yada labaran mataimakin Gwamnan Kano, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a.
A cewar Ibrahim, an fara yin jigilar ne a daren ranar Alhamis, inda aka kwashe daukacin alhazan, bayan sun samu kwanciyar hankali a sansaninsu na Mina.
Amirul Hajj na jihar wanda ya kasance mataimakin gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, kakakin majalisar dokoki ta jaha Jibril Falgore, yan majalisar dokokin jihar, shugaban ma’aikata Alhaji Abdullahi Musa na daga cikin wadanda suka isa sansanin alhazan na Mina
A nasa jawabin, Daraktan ayyukan Haji na hukumar Alhaji Kabir Muhammad Panda, ya ce an samar da kayyaki ga kowane mahajjaci da suka hada da sabulu, tabarma, man goge baki, da sauran kayan masarufi a tantuna.
“Don tabbatar da tsaro da tsari, maniyyatan da hukumar ta ba su katin shaida ne kawai za a ba su izinin shiga tantin alhazan Kano” baya ga katin shaidar NUSUK’ Inji Panda
A cewarsa, tawagar da aka tura a Muna, ta kunshi masu wa’azi, ma’aikatan lafiya da jagororin jin dadin jama’a, da kuma mambobin kwamitin tsaro. Ya kuma kara da cewa tawagar da za ta yi gaba za ta wuce Arafat da tsakar daren Juma’a don yin irin wannan shiri da zai saukaka gudanar da aiki ba tare da wata matsala ba.
Haka kuma, an ga mataimakiyar kwamandan Hisba bangaren mata, Dr Khadija Sulaiman, ta shagaltu da shirya mata cikin tsari a cikin sansanin Mina.
Zuwan alhazai a Mina wani muhimmin ci gaba ne a aikin hajjin, wanda ke jan hankalin miliyoyin alhazai daga sassan duniya a duk shekara.
Mina tana rikidewa zuwa babban birni na tanti, tana ba da masauki na ɗan lokaci, kula da lafiya, abinci, ruwa, da sauran muhimman ayyuka. Yayin zamansu a Mina, mahajjata za su yi salloli daban-daban da suka hada da Azahar, La’asar, Maghrib, Isha, da Asuba, kamar yadda Annabi ya yi.
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta ba da tabbacin samun jin dadi da walwala ga dukkan mahajjata.