Alhazan da suka fito daga Karamar Hukumar Gwale, sun bayyana matukar farin cikinsu bisa kokarin jami’in Kula da Aikin Hajji na yankin bisa kwazonsa.
A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar Alhazai ta Kano, Sulaiman Abdullahi Dederi ya fitar, yace daya Daga cikin Dattawan Alhazan yankin Alhaji Hudu Isma’il Shehu, shiya bayyana hakan Lokacin da yake Mika mukullin mota kyauta kirar Toyota Camry ga jami’in a dakin taron yankin
Alh, Hudu Isma’il Shehu, ya bayyana cewa a tarihin Karamar Hukumar ba’a taba samun jami’in Daya Kula da Alhazan yankin kimanin 175, zuwa kasa maitsarki ba tare da wata matsala ko korafi ba .

Alh, Hudu Isma’il, ya Kara da cewa irin wannan kokari Abun a yabane shiyasa ya Samar da wannan kyauta domin koyi ga yan’baya.
A nasa bangaren, Jami’in Kula da Aikin Hajji na Karamar Hukumar Gwale,Alh, mujitafa Muhd Auwal , ya baiyana matukar godiyarsa ga Wannan kyauta da Kuma karramawar da Alhazan suka shirya Masa.
Alh, Mujitafa Muhd Auwal, yace wannan kyauta ita ce irinta ta farko a tarihin rayuwarsa , wacce ba zai taba mantawa da ita ba.
Daga nan sai ya godewa Jagorancin hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, karkashin Babban Daraktan gudanarwar hukumar Alh, Lamin Rabi’u Danbappa, Wanda yace bisa kokarin sane ya Sami dukkanin nasarorin Daya cimma a yankin nasa.
Alh, Mujitafa Muhd, sai yayi Addu’ar Allah ya sakawa Alh, Hudu Isma’il Shehu da mafificin Alkhairi bisa wannan tagomashi.