Daga: Ibrahim Abubakar Nagarta
Na rubuta wannan takarda ne a matsayina na musulmin Nijeriya da ya damu, dangane da yadda ake samun hauhawar farashin hajji a Nijeriya, a duk shekara.
Lokaci ya yi kuma ya zama wajibi a wannan lokaci da al’amuran tattalin arziki ke ci gaba da tabarbarewa ga mafi yawan ‘yan Nijeriya masu hankali da tausayawa da son yardar Allah su yi kira da kiraye-kirayen ga kamfanonin jiragen sama da za su yi jigilar alhazan Nijeriya don aikin hajjin 2025, don yin la’akari da rage farashin tikitin jirgin sama, daga dala $2000 a halin yanzu zuwa akalla $ 1500 ko kasa da haka a kan kowa, kuma a bar alhazai su biya kudin gida a kudinmu na gida wato (Naira).
Tabbas, idan aka yi haka hakika za a samu ramgwame wajen rage tsadar kudin aikin hajji a kasar, ta yadda za a samu damar samun dimbin mabiya addinin muslunci su samu damar gudanar da aikin hajji.
Duk da cewa su kansu kamfanonin jiragen sama suna biyan wasu haraji ko caji ga hukumar kula da filayen jiragen sama ta tarayyar Najeriya (FAAN) da sauran hukumomi, domin sauka da tashin jirgi kamar Naira 25,000 ga duk wanda ya sauka da tashin, kaso 15% na tikiti da kaya. Harajin samar da ci gaba da sauransu. Sai dai duk wadannan harajin da aka hada su bai kamata su sa a rika biyan makudan kudin tikitin da ake yi wa alhazanmu ba.
Idan dai za a iya tunawa, Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON, ta riga ta kafa wani kwamiti mai karfi da ke da alhakin tantance kamfanonin jiragen da za su gudanar da aikin hajjin na 2025 mai zuwa, tare da fito da mafi cancanta da kuma aiki da su.
Kamfanonin jiragen sama masu inganci a shirye suke su samar da ayyuka masu inganci ga alhazan Najeriya. Don haka, ina so in ba wa waɗanda za su yi zaɓi na ƙarshe na kamfanonin jiragen sama, a matsayina na ɗan ƙasa da su haɗa da batun rage kuɗin tikitin.
A ƙarshe, ya kamata sauran masu yin hidima ga alhazai na kowane nau’i su haɗa kai da juna a cikin kokarin da ake yi don samar da agaji ga mahajjatan Najeriya ta hanyar sake duba yadda za a taimaki alhazan Najeriya
Ibrahim Abubakar Nagarta, ya rubuto daga Kaduna