Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Usman, ya yi alkawarin karfafa hadin gwiwar hukumar da masu kamfanonin jigilar aikin Haji da Umra ta kasa domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji ba tare da wata matsala ba.
Ya yi wannan alkawarin ne a yayin bude sabon ofishin kungiyar masu aikin Hajji da Umrah ta Najeriya (AHUON) a Legas yau.
Farfesa Usman ya kuma bada tabbacin Hukumar ta NAHCON cewar a shirye take ta magance manyan kalubale musamman wadanda suka shafi bayar da bizar Umrah.
Da yake jawabi a wajen taron, kwamishinan ayyuka na NAHCON, Anofiu Elegushi, ya bayyana cewa hukumar ta kammala tantance kamfanonin da suka nemi lasisin aikin hajjin 2025.
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Amintattu na AHUON, Abdulfatai Abdulmajeed, ya nuna jin dadinsa ga NAHCON bisa irin tallafin da take baiwa Hukumar, ya kuma sha alwashin samar da hadin gwiwa mai inganci da Hukumar.