Hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON a karkashin jagorancin shugabanta Farfesa Abdullahi Saleh Usman ta fara shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin 2025.
An fara aikin ne da ziyarar aiki a kasar Saudiyya a ranar 7 ga watan Junairu, 2025, biyo bayan gayyatar da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta yi masa.
Hajj Chronicles Ta Taya Shugaban Hukumar NAHCON Murnar Cika Kwanaki 100 A Ofis
Wannan ziyarar na da nufin kammala rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna ta aikin hajjin 2025 da kuma karfafa wasu muhimman tsare-tsare na aikin hajjin na wannan shekara
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mataimakiyar daraktar yada labarai da dab’I ta hukumar, Fatima Sabda Usara, ta ce hukumar alhazai ta kasa NAHCON a karkashin jagorancin shugabanta Farfesa Abdullahi Saleh Usman ta fara shirye-shiryen tunkarar aikin Hajin 2025
An fara aikin ne da ziyarar aiki a kasar Saudiyya a ranar 7 ga watan Junairu, 2025, biyo bayan gayyatar da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta yi masa.
Wannan ziyarar na da nufin kammala rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin hajjin 2025 da kuma karfafa wasu muhimman tsare-tsare na aikin hajjin bana.
Tawagar NAHCON ta kunshi kwamishinonin tsare-tsare, bincike da kididdiga (Prof. Abubakar Abubakar Yagawal);
Ayyuka (Prince Anofiu Olanrewaju Elegushi); da Kudi (Alhaji Prince Aliu Abdulrazaq) Wakilan Hukumar Jin Dadin Alhazai na jahohi da masu kamfanonin jirgin yawo da masu ruwa da tsaki daga Majalisar Dokoki ta Kasa, da Fadar Shugaban Kasa, da kuma bangaren sufurin jiragen sama na cikin tawagar.
Wani muhimmin al’amari a yayin ziyarar shi ne, taron kasashen biyu da rattaba hannu a kan aikin Hajjin 2025, wanda aka shirya gudanarwa a ranar 12 ga watan Janairun 2025.
Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ministan harkokin wajen Najeriya, zai sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin Najeriya.
Bayan haka, tawagar za ta halarci bikin baje kolin alhazai na kasa da kasa a ranar 13 ga watan Junairu, 2025, inda za su yi la’akari da masu ba da hidima ga alhazan Najeriya.
A shirye-shiryen rattaba hannu kan yarjejeniyar, Farfesa Saleh da tawagarsa za su yi ganawa mai mahimmanci tare da jami’an ofishin jakadancin da na alhazai daban-daban, ciki har da masu yin ragistar aikin Haji, da wakilai daga Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama (GACA), da shugabanni na ayyukan Hajji na wasu kasashe.
Wadannan alkawuran za su biyo bayan rattaba hannu kan kwangila tare da manyan masu samar da ayyuka, kamar United Agents, Car Syndicates, Tafweej, da Adillah a Madina.
A lokaci guda ma’aikatan hukumar NAHCON suna gudanar da aikin duba wuraren kwana, da abinci da kuma wuraren kiwon lafiya a Makkah da Madina domin tabbatar da bin ka’idojin da ake bukata kafin a kammala yarjejeniyar.