A wata sanarwa da kakakin hukumar Mohammed Lawal Aliyu ya fitar, ya ce sabon wa’adin ya biyo bayan gyara da hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta yi na kalandar shekara ta 2025 inda ta umurci hukumomin jin dadin alhazai da na jihohi da su fitar da dukkan kudaden da aka karba kafin ranar 1 ga watan Fabrairu.
Sanarwar ta bayyana cewa kawo yanzu hukumar ta siyar da sama da kashi 40 na kujerun da aka ware mata na aikin Hajjin bana tun bayan fara rajistar a watan Satumban bara.
Ya yi kira ga maniyyatan da su yi amfani da damar da suka samu wajen yin ajiya don aikin hajjin kafin sabon wa’adin yak are don cin gajiyar ayyukan da Hukumar ke yi a ayyukan Hajji.
Mai Magana da yawun hukumar ya bayyana cewa masu shirin zuwa aikin Hajji za su saka mafi karancin Naira Miliyan Takwas da Dari Hudu (N8, 400,000.00) ta hanyar Cakin banki daga duk wani banki na kasuwanci da zai biya Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Abuja don neman kujerarsu a Majalisun yanki da kuma babban ofishin hukumar dake a tsakiyar Abuja, har zuwa lokacin da hukumar za ta fitar da ainihin kudin aikin Hajjin.
Ya jaddada cewa an fara yin rajistar ne ta hanyar cakin Banki wanda ya yi daidai da ka’idar yin adalci a ayyukan mazauna yankin.
Sanarwar ta bayyana cewa maniyyatan da suka yi ajiya amma ba su iya zuwa aikin hajjin baya ba kuma har yanzu suna da kudinsu a wurin hukumar su tabbatar sun cika kudin don isa mafi karancin ajiya kafin sabon wa’adin yin rajistar ya kure.
Ya kuma jaddada shirye-shiryen hukumar na kara zage damtse wajen inganta ayyukan alhazai da suka yi rijista ta hanyar sabbin dabarun da aka bullo da su na aikin Hajji mai zuwa.