Kafofin yada labarai na al’ada da sauransu, sun kwashe tsawon sa’o’i 48 ko fiye da haka suna jin dadin sanarwar karshe na kudin Hajjin 2025 da shugaban hukumar alhazai ta Najeriya Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya sanar.
Idan dai za a iya tunawa, makwanni biyu da suka gabata, Farfesa Abdullahi Sale, yana kasar Saudiyya tare da tawagarsa wadanda suka hada da manyan masu ruwa da tsaki a harkokin aikin Hajji, suna kokarin shirya hanyoyin da za a bi don inganta yadda za ayi aikin Hajjin 2025 cikin nasara sosai, mai cike da lada, marar tsada fiye da a aya na ayyukan Hajji da suka gabata ba tare da wani gagarumin karin tsadar kudin aikin hajji ba idan aka kwatanta da na 2024, wanda shi ne Karin kudin da aka taba samu a tarihin aikin hajji a Najeriya.
Hakika, kafin bayyana kudin aikin hajjin 2025 na baya-bayan nan, akasarin ‘yan Nijeriya, musamman wadanda ke da niyyar shiga aikin hajjin bana, sun yi imani da yakinin cewa, idan aka yi la’akari da yadda canjin Naira zuwa Dala yake yi a halin yanzu. sannan akasin haka, kudin aikin Hajji zai kai Naira Miliyan Goma ko ma sama da haka, amma Alhamdulillahi, hasashe yanzu an tabbatar da cewa ba daidai ba ne bisa la’akari da hangen nesa da matakan da Shugaban Hukumar NAHCON da tawagarsa suka dauka cikin gaggawa, ta hanyar tattaunawa akai-akai tare da yin mu’amala da ma’aikatu daban-daban kamar masauki, da jiragen sama da dai sauransu, wanda ya haifar da sakamako mai kyau ta hanyar dakile kudin aikin hajji zuwa matakin da ya kai na kasa da Miliyan 9 a halin yanzu, sabanin Naira miliyan 10 da ‘yan kasar da dama suka yi hasashe.
Dole ne a yaba wa mataimakin shugaban kasa, mai girma Kashim Shettima saboda ya taka rawar gani wajen baiwa hukumar NAHCON duk goyon baya da shawarwari wanda ya kai ga samun nasarar wannan abin yabawa.
A saboda haka kungiyar tallafawa alhazan Najeriya ta kafafen yada labarai ta Najeriya (Nigerian Hajj Media Support Team) , na farin cikin bin sawun sauran ‘yan Najeriya masu kishin kasa domin rokon gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar sake tallafawa maniyyatan bana ta hanyar ba da rangwame don don bawa Karin musulmin Najeriya dammar halatar aikin Haji a rayuwarsu
Sa hannu
Ibrahim Abubakar Nagarta
Shugaban Tawagar ‘Yan Jaridu Masu Tallafawa Aikin Haji A Najeriya