Gwamnan Jihar Kaduna, Mai Girma Sanata (Dr) Uba Sani, ya nada Mai Martaba Sarkin Kauru, Mai Martaba Alhaji Ya’u Shehu Usman a matsayin Amirul Hajj kuma jagoran tawagar gwamnati don gudanar da aikin Hajjin 2025.
Hukumar Alhazai Ta Kaduna Ta Fara Mayar Da Kudade Ga Alhazan Da Suka Halarci Aikin Hajin 2023
A sanarwar da Sakataren yada labaran Gwamnan Ibrahim Musa Babba ya sanyawa hannu, yace Nadin basaraken gargajiyar da ake mutuntawa ya dogara ne da tarihinsa na sadaukar da kai, rikon amana da gudanar da harkokin dan Adam mai inganci.
Ana sa ran Amirul Hajj zai yi aiki kafada da kafada da kwamitin alhazai na jihar Kaduna, da sauran hukumomi a matakin jiha, tarayya da na kasa da kasa, domin gudanar da aikin hajjin na shekarar 2025 ba tare da samun wata matsala ba
A yayin da yake taya Amirul Hajji murnar wannan nadi da aka yi masa, Gwamna Uba Sani ya bukace shi da ya yi amfani da kwarewarsa na jagoranci domin ci gaba da gudanar da sabon aikin. Ya yi masa fatan Allah shiriya da tsari.
Ibrahim Musa
Babba
n Sakataren Yada Labarai