Daga Ismail Yusuf Makwarari
Shugaban hukumar kula da aikin Hajji ta Nijeriya sheikh Abdullahi Sale Usman, ya bayyana hakan cikin wani shiri na musamman da aka yi da shi kai tsaye a gidan talabijin na Africa TV3 a jihar Kano.
Shirin da babban daraktan tashar , Dr. Tijjani ya gabatar, ya mayar da hankali ne kan irin shirye-shiryen da hukumar ke gabatarwa gabanin fara jigilar Alhazan Nijeriya, zuwa ƙasa mai tsarki a watan mayu mai kamawa.
Sheikh Abdullahi Sale ya ce, ba shi da burin da ya fice ganin alhazan Nijeriya sun gudanar da aikin Hajji cikin farin ciki da walwala da kuma jin daɗi ba tare da wata matsala ba.
” Hakika zan yi amfani da kwarewa dana samu a baya, lokacin da na rike shugaban hukumar aikin Hajji ta Kano, da aikin Hajji dana gabatar a baya, lokacin gudanar tsare – tsaren da suka kamata. Misali, ” Batun masaukin alhazai da abincinsu da kuma uwa uba zaman Minna da kusan a nan ne ake fuskantar matsala. Kamar yanayin wurin kwana, ban daki, abinci dama ita kanta shemar da alhazan za su sauka.
Allah cikin ikonsa a halin yanzu, mun tanadi masauƙi na maniyyata kimanin dubu hamsin da biyu (52000) ƙarƙashin jihohi. Sai dubu ashirin da muka warewa masu jirgin yawo wato (Tour Operators).
Cikin shirin da muka yi da masu kula da masauƙan alhazanmu a Minna da Arfa, shi ne za a samar da wadatattun ban dakuna da sauran abubuwan da suka kamata domin jin dadin alhazanmu”.
“Wani abin albishir, da na ke son bayyaanawa a nan shi ne yadda muka samarwa alhazai ragin kuɗi cikin kuɗaɗen da alhazan Nijeriya za su biya a wannan shekara ta 2025 da adadin ya kai naira biliyon hamsin da huɗu ( 54), wanda hakan ya taimaka wajen sauƙaƙa kuɗin kujerar zuwa aikin Hajji. Duk da farashin Dala da ya tashi. muna godiya ga Allah(S.W.A)”.
Ko da aka tambayi Sheikh Abdullahi Sale kan batun kula da lafiyar Alhazai kuwa sai ya ce ” Hakika mun yi tanadi matuka,, tare da tsare – tsare kuma a nan zan yi amfani da wannan dama domin yin godiya ga ministan lafiya, bisa goyon baya da yake ba mu domin tabbatar da samar da duk wani abu da ake buƙata, domin kula da lafiyar alhazanmu, sannan za mu yi ƙoƙari wajen ganin mun samar da kwararrun jami’an lafiya da magunguna , da ma motocin ɗaukar marasa lafiya.
Bayan haka za mu cigaba da wayar da kan alhazanmu a kan rahoton da aka samu cewa, a bana za a samu yanayi na zafin rana, domin tabbatar da sun kiyaye dukkan shawarwarin da masana a harkokin lafiya suke bayarwa”.
Amma duk da wannan ƙoƙari da muka yi cikin ƙanƙanin lokaci har ake samun wasu suna yaɗa labaran da ba su da tushe a kan cigaban da muka samar cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Kuma a nan nake kira ga waɗanda suke amfani da kafaken yaɗa labarai suke sukar aikin da muke gudanarwa kan su dinga bayar da sahihan bayanai a kan hukumar aikin Hajji ta Nijeriya tare da tuntubar mu domin samun bayanai kafin yaɗawa.
Ina ƙara jaddada manufata da kuma kudirina na tabbatar da cewar, Alhazan Nijeriya sun samu walwala kuma sun yi ibadar aikin Hajji cikin jin dadi domin shi ne burina”.
Sannan ina godiya ta musamman ga hukumomin jin daɗin alhazan Jihohi, bisa yadda suka bayar da goyon baya da suka bayar kan samarwa alhazai masauƙi da masu samar musu da abinci, in sha Allah, babu wanda zai yi ƙorafi a kai.
Sannan ya godewa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da Mataimakinsa Shatima Kashim bisa gudunmawar da sukr bayarwa wajen samun nasarar aikin Hajjin wannan shekara ta 2025.