A wani abin alfahari a harkar gudanar da aikin Hajji, Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta samu nasarar jigilar kashi goma sha tara cikin dari (19%) na ‘yan Najeriya da ke shirin sauke farali a shekarar 2025 cikin kwanaki uku kacal tun bayan fara aikin jigilar.
Wannan gagarumar nasara ta janyo yabo daga masu ruwa da tsaki da dama a fannin aikin Hajji, inda da dama ke danganta nasarar da kokarin sabon shugabancin hukumar karkashin Farfesa Abdullahi Saleh Usman.
Daidaito da tsari mai kyau wajen gudanar da jigilar mahajjata daga sassa daban-daban na kasar ya nuna sabuwar azama da jajircewar hukumar wajen kula da walwalar alhazan Najeriya. Wannan nasara ta kuma nuna kyakkyawan farawa ga aikin Hajjin bana, tare da kara karfafa gwiwar alhazai, kamfanonin Hajj, da sauran abokan hulɗa na kasa da kasa.
Masana na ganin cewa wannan ci gaba ya yi daidai da alkawarin NAHCON na fara jigilar mahajjata da wuri, bisa ga sabon tsarin da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fitar don inganta aikin Hajji a duniya baki daya.
Majiyar da ke kusa da hukumar ta bayyana cewa wannan nasara ta samu ne sakamakon tsare-tsare tun da wuri, hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki, da kuma amfani da tsarin sa-ido na zamani dukkansu sun taka muhimmiyar rawa wajen cimma wannan matsayi.
Yayin da shirin Hajjin ke ci gaba, idanu na kan NAHCON don ganin ta ci gaba da wannan turbar nasara domin tabbatar da aikin Hajji mai tsafta da kwanciyar hankali ga dukkan alhazan Najeriya.