Bayan da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fitar da jadawalin aikin Hajji na shekarar 2026 (1447 AH), Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta dauki wannan jadawali a matsayin tubali na tsara Hajjin duniya baki daya cikin tsari da haske dama ce ga kowace kasa ta shirya yadda ya kamata.
Wannan jadawali na aiki da Ma’aikatar Hajjin Saudiyya ta fitar ba kawai takarda ce ba tsari ne da ke da nufin daidaita aikace-aikacen Hajji na kasashe da tsare-tsaren duniya na zamani.
Yanzu kuma lamarin yana hannunmu.
Jadawalin da Saudiyya ta fitar, tare da saukaka shi da NAHCON, ya ƙunshi muhimman matakai guda bakwai daga wayar da kai da sanya hannu kan kwangiloli tun da wuri, zuwa jigilar Alhazai daga watan Afrilu 2026. Wadannan matakai ba kawai takardun aiki ba ne maki ne da idan aka bata lokaci a kowane mataki, hakan zai iya kawo cikas ga dubban Alhazai.
Kowane mataki yana da muhimmanci. Kowace rana wata alkawari ce. A wannan karon, dole ne mu cika wannan alkawari.
Abin da wannan marubuci ya koya daga shekaru da dama yana kallon ayyukan Hajjin Najeriya shi ne: lokaci abu ne mai muhimmanci. Shiri tun da wuri ba kawai yana saukaka aiki ba ne, yana inganta jin dadin Alhaji kai tsaye.
Idan muka biya kudin Hajji da wuri:
Muna samun otal-otal kusa da Harami sauki ne ga tsofaffi da masu rauni.
Muna samun sansanin kwana masu inganci a Mina – musamman kusa da Jamrat.
Muna samun motocin sufuri da abinci masu kyau a farashi mai sauki.
Muna guje wa yanke shawara cikin gaggawa da saukin kamun aikin da yakan biyo bayan shirye-shiryen karshe.
A saukake, shiri tun da wuri yana nufin Hajji mai cike da mutunci da kwanciyar hankali.
Ba sai an je nesa ba wajen fahimtar illar jinkiri. Hajjin shekarar 2025 ta bar darasi mai radadi. Yayin da wasu Alhazai daga Najeriya suka riga suka biya kudinsu, sun kasa tafiya saboda an rufe portal na bizar Saudiyya daga bisani, babu karin lokaci, babu wani sassauci.
Abin takaici ne ganin mutane da suka shafe shekaru suna mafarkin Hajji an hana su tafiya saboda rashin daukar mataki tun da wuri.
Wannan ba batun manufofi bane kawai, batun jin kai ne.
Tsarin Ajiya Don Hajji:
Abin farin ciki, yanzu akwai wata hanya ta ajiye kudi cikin tsarin shari’a domin gudanar da Hajji, wato Hajj Savings Scheme – tsarin da NAHCON ke sa ido kai tsaye.
Za ka iya bude asusun ajiya na Hajji a daya daga cikin wadannan bankuna:
Jaiz Bank
Lotus Bank
TAJ Bank
Alternative Bank
Haka kuma, za a iya fara tsarin ta hanyar Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihohi, domin da dama daga cikinsu sun hada kai da wannan tsari.
Ba kawai sauki bane, hanya ce ta bai wa Alhazai dama su rarraba kudin, rage damuwa, da kuma gujewa jinkiri.
Hajji ba yawon bude ido bane. Daya ne daga cikin ginshikan Musulunci guda biyar tafiya ce ta sadaukarwa, ibada da zurfin ma’ana ga rai. Wasu daga cikin Alhazai na shafe shekaru masu yawa suna tara kudi don wannan tafiya ta rayuwa guda. Mafi karancin abin da za mu iya yi a matsayin masu ruwa da tsaki shi ne mu tabbatar ba za a hana su cimma burinsu saboda sakaci ko jinkirinmu ba.
Ba za mu iya ci gaba da aiki kamar yadda muka saba ba. Lokaci ya kure.
Bin wannan jadawali ba kawai cika wa’adin lokaci bane hanya ce ta samun fa’ida kai tsaye:
Samun mafaka kusa da wuraren ibada
Ingantaccen wurin kwana a Mina
Saukaka wajen sarrafa biza da tafiya
Rage kudade saboda shirye-shiryen da aka yi tun da wuri
Samun lokaci mai yawa don horar da Alhazai
Fiye da hakan, yana nuna cewa Najeriya ma za ta iya yin abin da ya dace tsarinmu yana aiki idan an bi shi.
Hanyar zuwa Hajjin 2026 ta riga ta fara. Muna da jadawalin lokaci. Muna da bankuna. Muna da tsari. Abin da ya rage shi ne niyyar mu baki daya yanzu, ba daga baya ba.
Idan muka hada kai NAHCON, hukumomin jihohi, kamfanonin Jirgin yawon da Alhazai kansu, za mu iya gujewa rikice-rikicen da suka gabata, mu kuma samar da aikin Hajji da ya dace da darajar addinin Musulunci: tsari, girmamawa, tausayi, da nagarta.
Domin Hajji ba kawai tafiya ce ta jiki ba – tafiya ce ta rai. Kuma kowace rai ta cancanci Hajji mai cike da kwanciyar hankali, ma’ana, da shiri na gari.