Umarnin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar kwanan nan ga Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) da ta gaggauta sake duba farashin kujerar Hajjin shekarar 2026 tare da rage shi, wani babban ci gaba ne da ya dace da manufar Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, wanda burinsa tun farko shi ne tabbatar da cewa aikin Hajji ya kasance mai araha ga dukkan Musulman Najeriya.
Umarnin Shugaban Kasa ya bukaci NAHCON da ta sake lissafa farashin kujerun Hajji domin ya nuna yadda Naira ta samu karuwa a kan Dala.
Wannan mataki na gwamnati ya zo a kan gaba, yana ceton maniyyatan Najeriya daga tsadar kujerar da aka sanar da ita tun farko, wadda aka kirga bisa “hasashen sauyin kudi na N1,550 a kan Dala daya. Farashin farko ya kasance tsakanin N8.1m zuwa N8.5m bisa ga yankuna daban-daban.
Ana sa ran sabon umarnin zai rage farashin zuwa kusan tsakanin N7.6m da N7.7m.
Murnar da Shugaban NAHCON ya nuna kan wannan labari abin fahimta ne, domin ya tabbatar da jajircewarsa wajen rage farashi da kula da walwalar maniyyata.
Tun daga lokacin da ya hau Shugabancin hukumar, Farfesa Saleh Usman ya sanya araha da ingantacciyar hidima ga maniyyata a matsayin babban ginshikin aikinsa.
Ko da yake sabon yinkurin rage farashin ya samo asali ne daga karfin Naira, ya ginu ne kan matakan rage kudi da shugabancin NAHCON ya riga ya dauka tun da farko.
Daya daga cikin manyan nasarorin da shugabancin ya cimma shi ne tanadin rangwame ga maniyyata ta hanyar samun saukin farashin hidima da ya kai kimanin Naira biliyan 19 gaba daya. An cimma hakan ne bayan samun rangwamen fiye da N200,000 kan kowane maniyyaci daga wurin masu yin hidima ga Alhazai a Saudiyya, abin da ya zama babban tanadi ga kusan maniyyata 66,000 da aka warewa Najeriya.
Wani babban abin alfahari kuma shi ne yadda NAHCON ta inganta tsarin kwangiloli, wanda ya taka rawar gani wajen nasarar aikin Hajjin 2025.
A wancan lokacin, tawagar Farfesa Saleh Usman ta yi gyara kan kwangilolin ayyuka domin su dace da adadin maniyyatan da aka yi rajista, mataki wanda ya hana asarar kudi da yawa kuma ya taimaka wajen rage farashin kujerar.
NAHCON kuma ta fadada tsarin Hajj Savings Scheme, inda shugaban ya kara karfafa tsarin ta hanyar hada kai da karin bankuna domin karfafa al’adar ajiya tun da wuri, don rage wahalar biyan kudi da lokaci daya.
Sai dai duk wadannan nasarori ba su samu ba tare da kalubale ba. Kudurinsa na samar da hidimomi masu inganci da araha ya taba shiga rikici da wasu masu muradun kansu.
Rahotanni na nuna cewa tsadar da aka bayyana a farko na iya da nasaba da matsin lamba daga wasu bangarori da ke da hannu a harkar kwangila, musamman batun zaben kamfani daya tilo da zai rika gudanar da ayyukan din Hajji.
Manufar Farfesa Saleh Usman tun farko ita ce a dauki kamfanoni da dama masu inganci domin gudanar da ayyuka, domin hakan zai haifar da gasa mai kyau wadda za ta rage kudi kuma ta inganta sabis ga maniyyata. Saboda haka, wannan umarnin Shugaban Kasa ya zama tamkar karfafa guiwa da kuma damar da za ta bashi damar kaucewa duk wata cikas ta son kai ko na birokrasiya wajen cimma manufar rage farashi bisa mafi kyawun canjin kudi.
Domin cika wannan buri, Shugaban NAHCON yana kokarin karfafa al’adar biyan kudi da wuri. Ya bukaci Jihohin da ke da Hukumar Jin Dadin Alhazai su tabbatar da cewa suna aika kudin maniyyata cikin lokaci.
Wannan yana da matukar muhimmanci domin hakan zai bai wa Babban Bankin Kasa (CBN) damar sayen kudin kasashen waje bisa farashin da ya inganta, wanda hakan zai tabbatar da ajiye kudi ga maniyyata.
An sanya ranar karshe ta biyan kaso 50% na kudin Hajji a ranar 8 ga Oktoba, 2025, yayin da cikakken biyan kudin zai kare a ranar 31 ga Disamba, 2025.
A fili yake cewa Farfesa Abdullahi Saleh Usman yana kan hanya madaidaiciya wajen gudanar da daya daga cikin ayyukan Hajji mafi nasara da araha a tarihin Najeriya. Jajircewarsa kan amfani da kudi cikin hikima tare da goyon bayan fadar Shugaban Kasa na nuna alamar cewa aikin Hajjin 2026 zai kasance mai tarihi wanda zai tabbatar da manufar samun sauki da ingantaccen sabis ga maniyyata.
Sirajo Salisu Jibia
Ya rubuta daga Japan.