HAJJIN 2025: NAHCON ta ƙaddamar da kwamitin mutum 32 don soma aikin tankade da rairayar jiragen da za su yi aikin dakon Alhazai da kayansu
Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ƙarƙashin jagorancin Farfesa Abdullahi Saleh Usman ta nuna, cikin ɗan kankanin lokaci, cewa sauye-sauyen tsari na hukuma da aka gina bisa ƙwarewa da gaskiya na iya inganta ayyukan hidimar jama’a da alhazai matuƙa.
Zaman jagorancinsa ya nuna kwarewa da kuma sanin ya kamata sannan da nuna zuhudu don yi wa Najeriya da Alhazanta hidima ta yadda za a ayaba a koda yaushe.
Ɗaya daga cikin fitattun nasarorin NAHCON a ƙarƙashin Farfesa Usman shi ne dawo da tsari da ladabi a cikin shirye-shirye da aiwatar da aikin Hajji. Daga fara tuntuba da hukumomin Saudiyya tun da wuri zuwa bin jadawalin lokaci ba tare da sassauci ba, Hukumar ta rungumi salon aiki na gaba-gaba wanda ya rage rikice-rikicen aikin gaggawa.
Wannan sauyi ya haifar da ingantacciyar daidaituwa a fannin jigilar jiragen sama, masauki, abinci da sufuri ga Alhazan Najeriya fannonin da a baya suka jawo suka daga al’umma.
Haka kuma, an ba da muhimmanci sosai ga gaskiya. Jagorancin Farfesa Usman ya ƙarfafa tsarin kulawa na cikin gida tare da inganta haɗin gwiwa da hukumomin jin daɗin Alhazai na jihohi da kamfanonin yawon buɗe ido masu zaman kansu. Bayyanannun ƙa’idoji, tsauraran sharuddan bin doka, da buɗaɗɗun hanyoyin sadarwa sun rage rashin daidaito tare da ƙara amincewa tsakanin masu ruwa da tsaki. Ga Alhazai kuwa, hakan ya samar da fahimta mai kyau, da kuma ingantacciyar kulawa gaba ɗaya.
An kuma sake ba da kulawa ta musamman ga ka’idojin lafiya da tsaro. Ta hanyar tilasta bin ƙa’idojin lafiya na Saudiyya da ƙarfafa gwaje-gwajen lafiya kafin tafiya, NAHCON ta ɗauki matakai masu muhimmanci wajen kare Alhazai da kuma martabar Najeriya a matsayin ƙasa mai ɗaukar nauyin aika Alhazai cikin tsari. Waɗannan matakai, ko da yake wani lokaci ba su jawo farin jini ba, sun nuna jagoranci mai fifita martaba da amincewa na dogon lokaci fiye da sauƙin ayi gaggawa na ɗan lokaci.
Bayan harkokin aiki kawai, Farfesa Usman ya sake mayar da NAHCON a matsayin hukuma mai daraja a fagen diflomasiyyar Hajji ta duniya. Ingantacciyar alaƙa da hukumomin Hajji na Saudiyya da masu samar da ayyuka ta ƙarfafa matsayar Najeriya wajen tattaunawa, tare da tabbatar da kyakkyawan rabon dama da ingancin ayyuka ga Alhazan Najeriya.
A taƙaice, nasarar NAHCON a ƙarƙashin Farfesa Abdullahi Usman ba ta tsaya ga sauƙaƙa gudanar da aikin Hajji kaɗai ba, illa kafa tsare-tsare, ƙa’idoji, da al’adun sauyi na gyara. Duk da cewa har yanzu akwai ƙalubale, yanayin da ake ciki yana nuna cewa harkokin Hajji na Najeriya na tafiya ne ta hanyar dorewa, ƙwarewa, da mayar da hankali ga jin daɗin Alhazai, samun nasara da ta cancanci yabo da ƙarfafawa.
Haka kuma, sashen Yaɗa Labarai da dab’i na NAHCON ya cancanci yabo saboda ƙwarewar da sashen ke nunawa, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen irin ma’aikatan da ke wannan sashe a ƙarƙashin jagorancin Fatima Sanda Usara, ya yi fice wajen tsayuwar daka, bayyana gaskiya, da daidaito a harkar gudanar da bayanai.
Salon aikinta na ƙwarewa mai natsuwa sannan kuma cike da sanin makamshin aiki, musamman a lokutan da jama’a ke neman bayanai akai akai, Ta jagoranci wannan sashe wajen fede biri tun daga kai har wutsi wajen bayyana gaskiya domin al’umma su san abinda ake ciki.
Sannan kuma akwai Mohammed Musa Danbaba, wanda rawar da yake takawa ta daidaita bayanai ta taimaka wajen tsarawa da sauƙaƙa yadda bayanai ke gudana a cikin gida, tare da daidaita saƙonni tsakanin sassa daban-daban domin tabbatar da fahimta ɗaya da inganci a sadarwar jama’a.
Gudummawar Ahmed Mu’azu, Mataimaki na musamman ga Shugaban Hukumar kan Harkokin Watsa Labarai, ta ƙara ƙarfafa wannan tsari ta hanyar bayar da goyon bayan dabarun kafafen yaɗa labarai da kuma tabbatar da cewa manufofin Shugaban Hukumar da fifikon ayyukan NAHCON suna fitowa fili.
Ma’aikata irin su Suwaiba Ahmad, Sani Shafi’i, da wasu da dama a cikin sashen na taimakawa manema labarai, musamman domin sanin abinda ake kullawa a hukumar da kuma inda ake warwarewa.
Mohammed Ibn Mohd, Marubuci ne mazaunin Abuja, Najeriya.
(PT Hausa)

