Daga Jamilu Adam Shugabanci na gaskiya ba ya rasa kalubale. A harkar hidimar jama’a, musamman a wata muhimmiyar hukuma kamar Hukumar Kula da Ayyukan Hajji ta Kasa (NAHCON), duk wani jagora mai ƙwazo na fuskantar bincike, matsin lamba da kuma, a wasu lokuta, yaɗa labaran ƙarya.
Tun bayan hawansa kujerar shugabanci, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, Shugaban NAHCON, ya nuna nagartattun siffofin shugabanci na gaskiya shugabanci da ya ta’allaka kan gyara, gaskiya, bin doka da oda, da kuma haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki. Manufarsa ita ce sake tsarawa da inganta tsarin aikin Hajjin Nijeriya domin ya dace da ka’idojin duniya, tare da kare martaba da jin daɗin alhazai.
Shugabanci Mai Hangen Nesa da Jarumtaka
Daya daga cikin manyan siffofin shugabancin Shugaban NAHCON shi ne jajircewarsa wajen yanke shawara masu amfani ga ƙasa, koda kuwa hakan zai takura wa wasu tsoffin tsare-tsare ko muradun wasu ƙungiyoyi. Sau da yawa, shugabanci mai neman gyara kan fuskanci adawa daga masu amfana da tsohuwar hanya, wanda hakan kan janyo yaɗa labaran da ba su da tushe.
Farfesa Usman ya tsaya tsayin daka kan bin doka, gaskiya da mutuncin hukuma, lamarin da ya taimaka wajen dawo da amincewar jama’a da masu ruwa da tsaki, tare da ɗaga darajar NAHCON a idon duniya.
Guguwar Labaran Ƙarya
A ‘yan lokutan nan, an ga yaɗuwar wasu labarai marasa tushe da ke ƙoƙarin nuna cewa ana fuskantar rikici ko gazawa a hukumar.
Wadannan labarai ba su dogara da hujjoji ko sahihan bayanai ba, illa dai ƙoƙarin rikitar da tunanin jama’a.
Ya dace a fahimta cewa bambancin ra’ayi kan manufofi, sauye-sauyen tsari, da sake fasalin aiki ba alamun gazawa ba ne, illa alamun shugabanci mai ƙarfi da sanin makama. Yin wa irin waɗannan abubuwa kallon rikici na cutar da hukuma ne, ba gyara ta ba.
Kariyar Allah da Bayyanar Gaskiya
Duk da hayaniyar labaran ƙarya, abu guda ya fito fili: gaskiya tana bayyana koyaushe. Kowanne zargi ya shuɗe bayan sahihan bayanai, hujjojin aiki da sakamakon da aka gani a fili.
Wannan tsayin daka ba na tsarin aiki kawai ba ne; mutane da dama na ganin kariyar Allah ce ga shugaba mai niyyar bautawa al’umma da gaskiya.
A hidimar jama’a, inda ake yawan fahimtar aiki ba daidai ba ko karkatar da maganganu, imani, gaskiya da daidaito su ne ginshiƙan da ke riƙe shugabanci.
Manufar Gyara ta Shugaba Tinubu da Kwanciyar Hankalin Hukuma
Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta nuna karara cewa tana fifita ƙwarewa, gyara da sakamako. Ana tantance hukumomi bisa aiki, ba jita-jita ba.
A halin yanzu, NAHCON na ci gaba da aiwatar da ayyukanta yadda ya kamata abin da ke nuna cewa shugabancin hukumar na nan daram.
Don haka, ya zama wajibi ga jama’a da masu ruwa da tsaki su bambanta tsakanin sukar gina kasa, wacce ke ƙarfafa hukuma, da kuma ƙirƙirar cece-kuce, wacce ke hidimar muradun kai.
Kammalawa
Ana gwada shugabanci na gaskiya ne a lokacin matsin lamba, ba lokacin jin daɗi ba.
Abin da ke faruwa a NAHCON a yau na nuna cewa jajircewa, imani da sadaukarwa ga hidimar jama’a sun fi ƙarfin duk wani ƙoƙarin karkatar da gaskiya.
Yayin da ake shirin ayyukan Hajji na gaba, al’ummar Nijeriya na buƙatar mayar da hankali, ƙwarewa da haɗin kai. Tarihi zai rika tuna da waɗanda suka yi aiki don ƙarfafa hukumomi kuma ya bar waɗanda suka nemi raunana su a baya.
Hajj Chronicles na ci gaba da jajircewa wajen bayar da rahotanni masu gaskiya, bin ka’idojin aikin jarida, da kare mutuncin harkokin Hajji da Umrah a Nijeriya.

