Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta bukaci dukkan alhazai masu shirin tafiya aikin Hajji a jihar da su kasance cikin shiri domin gudanar da gwajin lafiya da ake shirin fara wa nan ba da jimawa ba.
A sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Darakta Janar na Hukumar, Lamin Rabi’u Danbappa, ya yi wannan kira ne yayin wata ziyarar aiki da ya kai Cibiyar Bitar Alhazai da ke Karamar Hukumar Doguwa.
Ya jaddada muhimmancin halartar taron Bitar, inda ya bayyana taron a matsayin ginshikin nasarar aikin Hajji, saboda a nan ne ake koyar da alhazai yadda za su gudanar da ibadu da sauran ayyukan Hajji yadda ya dace.
Darakta Janar din, wanda Daraktan Wayar da Kai, Alhaji Murtala Lawan Sani ya wakilta, ya bayyana cewa manufar ziyarar zuwa Karamar Hukumar Doguwa ita ce duba yadda ake gudanar da Bitar alhazai tare da tabbatar da bin ƙa’idoji da dokokin da aka shimfiɗa.
Alhaji Murtala Lawan Sani ya kara da cewa duk wani maniyyaci da bai halarci gwajin lafiya ba, ba za a ba shi bizar Hajji ba. Don haka ya bukaci alhazai su dauki batun da muhimmanci, kasancewar sharadi ne na dole.
A nasa jawabin, mataimakin daraktan Sashen Ayyuka (Operations), Faruk Musa Sani, ya bayyana cewa aikin Hajjin shekarar 2026 ya bambanta da na shekarun baya, domin za a haɗa Biza da takardar shaidar gwajin lafiya kai tsaye a dandalin Nusuk ta hanyar zamani (digitally).
Saboda haka, ya yi kira ga dukkan alhazai da har yanzu ba su mika fasfo na kasa da kasa ba da su gaggauta yin hakan domin kauce wa barin su a baya.
A yayin wannan ziyarar aikin, tawagar ta kai ziyara cibiyoyin bitar alhazai da ke Karamar Hukumomin Doguwa da Tudun Wada

