Daraktan Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya yi kira ga maniyyatan da ke shirin zuwa aikin Hajji daga jihar da su kula da yadda za su yi amfani da kayayyakin da aka tanada musu a Ƙasa Mai Tsarki.
Hajj 2025: Hukumar Alhazai Ta Kano Ta fara Aikin Samar Da Biza Ga Maniyyata
Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar sa ta duba yadda ake gudanar da kwas ɗin horaswa na Hajji a cibiyoyi daban-daban a faɗin jihar.
A cewarsa, Hukumar ta tanadi gidaje ginin bene Guda biyu da zai iya ɗaukar maniyyata 3,205. Ya jaddada muhimmancin tsaftar muhalli a cikin da wajen wuraren da aka tanadar.
Wakilin Daraktan Janar a yayin ziyarar, mamba a Hukumar, Sheikh Tijjani Sani Maihula, ya bukaci dukkan maniyyata su halarci kwas ɗin horaswar Hajji domin samun ilimin da zai basu damar gudanar da aikin Hajji cikin nasara.
A nata jawabin, Daya daga cikin mamba a Hukumar, Hajiya Aisha Munir Matawalle, ta bayyana ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna, Alhaji Abba Kabir Yusuf, inda ta ce an riga an samar da muhimman abubuwa ga maniyyatan, kamar jakunkunan hannu, kayan sawa na maza da mata, da Abun hannu na shaidar maniyyata, waɗanda za a fara rabawa nan ba da jimawa ba.
Hajiya Aisha Matawalle ta kuma bukaci maniyyatan da su tuna da Jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya a cikin addu’o’insu a ƙasa mai tsarki.
A nasa bangaren, Daraktan Ilimi da wayar dakan Alhazai na hukumar, Alhaji Murtala Lawan Sani, ya ja kunnen maniyyata kan kaucewa ɗaukar kayan haramun ko waɗanda aka hana zuwa Ƙasa Mai Tsarki. Ya ce duk wanda aka kama da irin waɗannan kayayyaki, zai ɗauki alhakin abin da ya faru da kansa.
Alhaji Murtala Lawan Sani ya kuma godewa Daraktan Janar bisa shirya wannan ziyarar ta horaswa, wanda ya ce ta taimaka matuƙa wajen wayar da kan maniyyata.
Sauran da suka gabatar da jawabi yayin ziyarar sun haɗa da Daraktan Tsarin Ajiya na Hajji, Mataimakin Daraktan Sashen Bincike da Kuma Shugabar kula da sashen Lafiya na Hukumar.
Cibiyoyin da aka ziyarta sun haɗa da na Rimin Gado, Kumbotso da Dala a cikin ƙananan hukumomi na jihar.