A shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana, ma’aikatar harkokin cikin gida ta sanar da tsare-tsare da nufin kiyaye lafiyar mahajjata da ba su damar gudanar da aikin Hajji cikin sauki da kwanciyar hankali.
Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya ruwaito daga ranar 23 ga watan Afrilu mazauna masarautar da ke son shiga Makkah dole ne su sami izini daga hukumomin da abin ya shafa.
Ma’aikatar ta ce za a hana mutanen da ba su da cikakken izini shiga Makkah, kuma za a mayar da su inda suka nufa.
Ma’aikatar ta kara da cewa kebewa ya shafi mazauna da ke da takardar izinin aiki na wurare masu tsarki da hukumar da abin ya shafa ke bayarwa, ko wadanda ke da takardar shaidar zama da Makkah ta bayar, ko kuma wadanda ke da takardar izinin aikin Hajji.
Ana ba da izinin shiga ga mazauna da ke aiki a lokacin aikin Hajji ta hanyar yanar gizo ta (Absher Individuals) da (Muqeem portal) in ji SPA.
Hukumomin sun kuma dakatar da bayar da izinin Umrah ta dandalin Nusuk ga ‘yan kasar Masarautar, da kasashen yankin Gulf, mazauna cikin masarautar, da masu sauran biza daga ranar 29 ga Afrilu zuwa 10 ga watan Yuni.
Ba wanda ke da kowane irin biza da za a ba shi izinin shiga ko zama a Makkah – sai dai masu bizar Hajji – daga ranar 29 ga Afrilu, in ji ma’aikatar.
Tun da farko ma’aikatar ta sanar da cewa ranar karshe ga masu neman izinin Umrah za su shiga Masarautar ita ce ranar 13 ga watan Afrilu, kuma ranar karshe da za su fita ita ce 29 ga Afrilu, kamar yadda SPA ta ruwaito.
Kamfanoni da cibiyoyin hidimar alhazai da masu aikin Umrah wadanda suka kasa kai rahoton duk wani jinkiri ga hukumomin da abin ya shafa na iya fuskantar tarar kudi har SR100,000 ($26,600), tare da daukar matakin shari’a kan wadanda suka aikata laifin.
Za a ninka tarar ya danganta da adadin mutane nawa ne ke keta wa’adin tashi, a cewar SPA. Ma’aikatar harkokin cikin gida tana kira ga a bi ka’idojin aikin Hajji da kuma hada kai da hukumomin da abin ya shafa don tabbatar da tsaron alhazai.
(ARAB NEWS)