Murabus ɗin da Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya yi daga matsayin Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ya haifar da gibi a shugabanci a wani lokaci mai matuƙar muhimmanci.
Ko da yake murabus abu ne da ke faruwa a hidimar jama’a, jinkirin nada cikakken wanda zai maye gurbinsa na iya zama barazana ga kyakkyawan tsari da nasarar shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2026 a Jihar Kano.
Gudanar da aikin Hajji ba aiki ba ne da ake farawa watanni kaɗan kafin tafiya. Aiki ne na shekara gaba ɗaya wanda ke buƙatar tsari tun da wuri, haɗin kai, tattaunawa, da bin jadawalin lokuta da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da hukumomin Saudiyya suka tanada. Duk wani tangarda a shugabanci a wannan mataki na iya haifar da illa mai girma ga alhazan da ke shirin tafiya.
Jihar Kano, kasancewarta ɗaya daga cikin jihohin da ke da yawan alhazai a Nijeriya, ba za ta iya jure rashin tabbas a shugabancin Hukumar Jin Daɗin Alhazai ba. Batutuwan da suka shafi rabon kujerun Hajji, masauki, jigilar jirage, ayyukan lafiya, shirye-shiryen wayar da kai, tura ma’aikata, da al’amuran kuɗi na buƙatar ingantaccen tsarin jagoranci. Rashin cikakken Shugaban Hukuma na rage inganci da kuma sanya alhakin aiki ya zama mara tabbas.
Kwarewa ta nuna cewa jinkiri wajen yanke hukunci kan al’amura da dama yana iya janyo matsaloli da za a iya kauce musu a yayin aikin Hajji.
Darussa daga ayyukan Hajji na baya a faɗin ƙasar sun nuna cewa tsari tun da wuri, haɗin kai mai ƙarfi, da yanke hukunci a kan lokaci su ne ginshiƙan samun sauƙin biyan kuɗaɗe, ingantaccen masauki, da kyakkyawar walwalar alhazai. Kano na da damar amfani da waɗannan darussa domin kafa misali nagari a aikin Hajjin 2026.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna jajircewarsa wajen aiwatar da sauye-sauye, inganta aiki, da tabbatar da mulki mai mayar da hankali kan jama’a. Gwamnatinsa ta ba da muhimmanci ga ingancin ayyuka da ƙarfafa hukumomi a fannoni daban-daban.
Nada ƙwararren Shugaban Hukuma mai ƙwarewa da iya yanke hukunci cikin gaggawa ya dace ƙwarai da wannan hangen nesa, kuma hakan zai ƙara wa jama’a kwarin gwiwa kan yadda ake tafiyar da harkokin Hajji a jihar.
Bugu da ƙari, jadawalin ayyukan NAHCON ba ya jira jihohin da ke fuskantar sauyin shugabanci a ciki. Lokutan biyan kuɗaɗe, miƙa bayanai, da kulla yarjejeniya suna da tsayayyen lokaci.
Tsawaita rashin cikakken shugabanci na iya sa Kano ta samu koma baya a tattaunawa da masu samar da ayyuka a Saudiyya, wanda hakan na iya shafar ingancin masauki, abinci, da jin daɗin alhazai gaba ɗaya.
Bayan ɓangaren gudanarwa, akwai kuma ɓangaren ɗan-Adam. Dubban alhazai masu niyyar zuwa Hajjin 2026 sun riga sun fara tanadin kuɗi, yin rajista, da shirye-shiryen addini da na rayuwa. Sun cancanci samun tabbacin cewa harkokinsu na hannun shugabanci cikakke mai ikon yanke hukunci cikin lokaci.
Saboda haka, ya zama wajibi ga Gwamnatin Jihar Kano ta ɗauki mataki cikin gaggawa ta hanyar nada sabon Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai wanda ke da cikakken ilimi kan aikin Hajji, ƙwarewar gudanarwa, da iya aiki tare da NAHCON da sauran masu ruwa da tsaki.
Ci gaba da aiki ba tare da tangarda ba, ƙwarewa, da fara aiki tun da wuri su ne mabuɗan samun Hajji mai nasara.
A ƙarshe, jinkiri ba abu ne marar illa ba yana da sakamako. Kowame mako da aka yi ba tare da cikakken shugabanci ba, mako ne da aka rasa wajen shiri.
Don kare muradun alhazan Kano da kuma ci gaba da kyakkyawan sunan jihar a harkokin Hajji, ya kamata a ɗauki nadin sabon Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano a matsayin lamari na gaggawa.
Alhazan Kano sun cancanci ɗaukar mataki cikin hanzari dangane da abun da ya shafesu

