Dukkanin Ma’aikatan Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Sokoto suna cikin matsanancin alhini sakamakon rasuwar ɗaya daga cikin ma’aikatansu mai ƙwazo, marigayiya Nuratu Abubakar.
KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN: An Yi Addu’o’i Na Musamman a Madina Domin Zaman Lafiya da Ci gaban Jihar Sokoto
A cewar shugaban sashen yada labarai da sadarwa na hukumar, Faruku Umar, yace Shugaban Hukumar, Alhaji Aliyu Musa, tare da mambobin Hukumar, shugabanni da ma’aikata, sun halarci sallar jana’izar marigayiyar.
An gudanar da sallar jana’izar a Masallacin Juma’a na Sa’ad bn Waqqas, inda ɗaruruwan musulmi suka taru domin yi mata Sallah da addu’o’in neman gafara da rahama.
Shugaban Hukumar, Alhaji Aliyu Musa, ya bayyana marigayiya Nuratu Abubakar a matsayin ma’aikaciya mai jajircewa da ƙwazo, wadda gudummawarta za ta yi matuƙar tasiri.
Ya ce rasuwarta babbar rashi ce ba ga Hukumar kaɗai ba, har ma ga duk wanda ya santa.
Shugaban ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zamo makomarta, tare da bai wa iyalanta, abokanta da abokan aikinta haƙurin jure wannan babban rashi.

