A wani kwakkwaran bincike da kungiyar ‘yan jaridu masu Tallafawa Alhazan Najeriya ta yi kan musayar yawun da ke faruwa tsakanin bangarorin da aka ambata, na baya-bayan nan shi ne, hukumar alhazan Najeriya da kuma kamfanin samar da hidima na kasar Saudiyya dangane da yarjejeniyar kwangilar yin hidima ga Alhazan Nijeriya musamman a wurin Masha’ir, ya nuna cewa a gaskiya tun da farko NAHCON ta nuna sha’awarta da kuma shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji a Najeriya da kamfanin, amma daga baya Hukumar Aikin Haji ta Najeriya ta gano cewa, Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ba ta warware wasu muhimman batutuwan da suka shafi aikin Hajji da Umrah ba da kamfanin Al-Dhahabiah, kuma idan har ta yi kokarin kulla yarjejeniya da kamfanin a cikin wannan yanayin matakin na iya kawo cikas ga shirye-shiryen aikin Hajjin 2025 wanda ya kai ga ci gaba.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, Yace Babu Wani Maniyyaci Da Zai Rasa Zuwa Hajin Bana
Sai dai kuma hukumar ta NAHCON a karkashin Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ta bai wa Mashariq Al-Dhahabiah dammar wasu kwanaki da ya warware matsalolin da ya ke da shi a tsakaninsa da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya, wadda ke a matsayin hukumar da ke kula da duk wani kafanin dake hidimtawa, amma abin takaici, ta kai kamfanin a cikin tambaya kusan makwanni biyu kafin ya sanarwa da NAHCON, cewa ya warware duk wata tangarda da hukumomin da suka dace.
Har ila yau, sanannen abu ne cewa, ba wai kawai Hukumar Hajji da Umrah ta Saudiyya ba, duk wata babbar hukumar aikin hajji ko ma’aikatu kamar yadda lamarin ya kasance a duniya, ba za su kuskura su yi kasadar jinkirin yin sanya hannu kan kwangilar ma’aikatan da suka cancanta daidai lokacin da ya dace ba domin samun nasara kan wa’adin da ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta sanya,
A saboda haka cikin hikima dabasira ta shugaban hukumar ta NAHCON cikin gaggawa ya dauki matakin da ya dace, hana jinkirin da ba dole ba, wanda zai iya haifar da babbar matsala, wanda zai iya yin tasiri ga lamuni na aikin hajjin 2025, don haka, shawarar da Hukumar Alhazai ta kasa ta yanke na raba aikin kashi biyu tare da wani kamfanin yi wa alhazai hidima na Saudiyya, don samar da ayyuka masu nagarta ga Alhazan Najeriya kafin lokaci ya kure.
A saboda haka Kungiyar yan jaridu masu Tallafawa Alhazan Najeriya tana shawartar ‘yan jaridar da suke da dabi’ar yin watsi da ko kuma suka saba wa ka’idar tuntubar kowanne bangare da adalci a aikin jarida da su sake yin tunani tare da rungumar wannan muhimmin la’akari da da’a wajen gudanar da ayyukansu na kwararru, musamman idan bangarori biyu ko fiye suka shiga cikin wata matsala kafin a gaggauta sakin labarinsu.