Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya roki gwamnatin tarayya da ta rage kudin aikin Hajji duba da irin kalubalen da ‘yan kasa ke fuskanta na tattalin arziki.
Gwamnan ya yi wannan roko ne a yayin wani taron da hukumar jin dadin alhazai ta jihar ta shirya domin mayar da kudaden da gwamnatin Saudiyya ta bayar sakamakon matsalar wutar lantarki a lokacin gudanar da aikin Hajjin 2023.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Litinin.
Gwamnan ya kuma yabawa kokarin gwamnatin Saudiyya kan wannan karamci da nuna kulawa ga bil’adama.
Gwamnan yayi alkawarin aika wasikar godiya ga gwamnatin Saudiyya ta ofishin jakadancinsu dake jihar Kano.
Ya kuma nuna godiya ga hukumar alhazai ta kasa bisa tsantseni da biyan kudi akan lokaci.
Gwamna Yusuf ya bayyana jin dadinsa kan kokarin hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano na gudanar da aikin Hajji cikin nasara wanda aka amince da shi a matsayin mafi inganci a kasar nan.
Ya bukace su da su ci gaba da aiki mai kyau a ayyuka na gaba.
Gwamnan ya bayyana cewa ya ziyarci kasar Saudiyya ne a makonnin da suka gabata domin gudanar da aikin Umrah, sannan kuma ya fara shirye-shiryen aikin Hajji na gaba da kansa domin gano wuraren da Hukumar ke bukatar agajin gwamnati
A nasa jawabin mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo wanda shi ne jagoran alhazan Kano na shekarar 2024 ya yaba da irin tallafin da gwamna Yusuf ya baiwa alhazai kafin da lokacin da kuma bayan kammala aikin hajji.
Tun da farko, Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Laminu Rabiu Danbaffa ya ce jimillar kudaden da aka mayar wa jihar ta hannun hukumar alhazai ta kasa domin rabawa Alhazan da suka yi aikin hajjin 2023 Naira miliyan 375.