Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin Alhaji Abubakar Mawalle a matsayin Mukaddashin Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, a wani mataki na ƙara inganta tafiyar da harkokin aikin Hajji da Umrah a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
Alhaji Abubakar Mawalle ba baƙo ba ne a harkokin hukumar, domin ya taɓa riƙe muƙamin Sakataren Zartarwa (Executive Secretary) na Hukumar a lokacin gwamnatin da ta gabata, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen kula da walwalar alhazai da kuma tabbatar da nasarar gudanar da ayyukan Hajji.
Naɗin nasa, wanda ya fara aiki nan take, na nuna amincewar gwamnatin jihar da ƙwarewarsa, gogewarsa, da cikakken saninsa kan tsarin aikin Hukumar, musamman a wannan lokaci da ake buƙatar shugabanci mai ƙarfi domin shiryawa da aiwatar da ayyukan Hajji yadda ya kamata.
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana fatan cewa, a ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abubakar Mawalle a matsayin Mukaddashin Darakta Janar, Hukumar za ta ci gaba da ƙarfafa nagarta, gaskiya da ingantaccen hidima ga alhazan jihar, daidai da manufofin gwamnati na sauya fasalin harkokin Hajji.
Masu ruwa da tsaki sun yaba da wannan naɗi, suna bayyana shi a matsayin wanda ya zo lokacin da ya dace kuma abin ƙarfafawa, musamman ganin irin gogewa da Abubakar Mawalle ke da ita a harkokin Hukumar da kuma ayyukan gwamnati kasancewasa tsohon babban Sakatare a gwamnatin Kano, wanda ke ba da tabbacin daidaito da inganci a tafiyar da ayyukan Hajji a jihar.

