Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Jigawa ta ce ta mikawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON kudaden aikin hajjin maniyyatan jihar na shekarar 2025 kimanin naira Miliyan Dubu huɗu da miyan Dari Biyar.
Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar.
Hukumar Jin Dadin Alhazan Jihar Jigawa Za Ta Mayar Da Naira Miliyan 95 Ga Alhazan Hajin 2023
Darakta Janar ya ce hukumar ta aika wa NAHCON Naira Miliyan Dubu Huda da Miliyan Dari Biyar da Ashirin (4.520), a yayin da take sa ran za ta kara biyan wasu kudaden kafin cikar wa’adin da NAHCON din ta bayar.
Ya bayyana cewa hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta baiwa jihar kujeru 1,809.
A cewarsa Umar Labbo, tuni hukumar ta raba kashi 40 cikin 100 ga kananan hukumomin jihar domin gudanar da aikin hajjin bana.
Don haka Labbo ya bukaci Maniyyatan jihar ta Jigawa da su gaggauta kammala biyan kudaden su kafin wa’adin da NAHCON ta bayyana, saboda rashin yin haka na iya sa su rasa kujerunsu.
Ya kuma bayyana cewa nan ba da dadewa ba hukumar za ta fara gudanar da taron bita ga maniyyata a cibiyoyin da wasu Malamai suka kebe domin alhazan jihar.
Yayin da yake tsokaci kan masaukin Alhazai, Labbo ya ce hukumar ta samar da masauki na alfarma kusa da Masallacin Harami da ke birnin Makkah, domin alhazan jihar su sami damar gudanar da ayyukansu cikin sauki.
Haka zalika ya bukaci maniyyatan da su ci gaba da bai wa hukumar hadin kai domin cimma burin da ake so.
Tun da farko dai hukumar ta sanar da sama da Naira miliyan 8 da Dubu Dari Hudu a matsayin kudin aikin Hajjin shekarar 2025 ga maniyyatan jihar.
A karshe Umar Labbo ya yaba da irin goyon baya da kuma kyakkyawar alakar aiki da ake samu a tsakanin mahukuntan hukumar da ko’odinetoci, inda ya yi addu’ar samun dauwamammen hadin gwiwa domin amfanin kowa da kowa da kuma ci gaban jihar ta Jigawa.