Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta fara aikin tantancewa kamfanonin Jirgin yawo masu zaman kansu, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryenta na gudanar da aikin Umrah da Hajj na shekarar 2026.
Aikin tantancewar ya biyo bayan ƙaddamar da kwamitin tantancewa da bayar da lasisin kamfanonin jirgin yawo masu zaman kansu da Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yi a makon da ya gabata a Abuja.
An bai wa kwamitin umarnin tantance da nazarin dukkan aikace-aikacen da kamfanoni masu neman lasisi ko sabunta lasisi suka gabatar, domin samun damar shiga cikin shirye-shiryen aikin Hajji na gaba.
An fara gudanar da aikin tantancewar a Jihar Kano, inda tawagar daga Sashen Kamfanonin Jirgin Yawo na Hukumar (Tour Operators Unit) ƙarƙashin sashen Ayyuka, Dubawa da Lasisi (OILS) ke jagoranta.
Tawagar tana ziyartar ofisoshin kamfanonin Jirgin Yawo don duba kayayyakin aikinsu, takardunsu, ma’aikatansu da kuma yadda suke bin ƙa’idojin aiki da Hukumar ta gindaya.
Yayin kaddamar da fara aikin, wani wakili na Hukumar ya bayyana cewa manufar tantancewar ita ce tabbatar da cewa kawai kamfanoni masu inganci, ƙwararru kuma masu ƙarfi a ɓangaren kuɗi ne za su samu lasisin gudanar da aikin Hajji da Umrah na shekarar 2026.
“Wannan tsarin yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana, da inganci. Yana tabbatar da cewa kawai waɗanda suka cika ƙa’idojin Hukumar da na hukumomin Saudiyya ne za su samu izinin gudanar da aiki,” in ji jami’in.
Farfesa Abdullahi Saleh Usman, yayin ƙaddamar da kwamitin a baya, ya jaddada cewa Hukumar za ta tsaya kai da fata wajen tabbatar da bin ƙa’ida, yana mai cewa sahihancin aikin Hajji da Umrah na Najeriya yana ta’allaka ne da inganci da gaskiyar kamfanonin balaguro masu lasisi.
Ana sa ran aikin tantancewar zai ci gaba zuwa sauran yankunan ƙasar nan a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, domin ya shafi dukkan kamfanonin balaguro masu rajista da masu neman sabunta rajista a fadin ƙasa.
Ta hanyar wannan aiki, NAHCON ta sake tabbatar da kudirinta na ƙarfafa tsari da kulawa, tare da tabbatar da cewa dukkan alhazai ‘yan Najeriya ko ta ofishin jihohi ko ta kamfanonin jirgin yawo masu zaman kansu sun sami ingantaccen hidima da kariya a lokacin gudanar da aikin Hajji da Umrah na shekarar 2026.