- Gwamnatin jihar Osun ta kaddamar da hanyoyin yin rijistar maniyyata domin gudanar da aikin hajjin bana na shekarar 2025 zuwa kasashen Saudiyya da Isra’ila.
Wata sanarwa da kwamishinan harkokin cikin gida na jihar, Rasheed Aderibigbe ya samu a Osogbo ranar Talata, ta ce an dauki wannan matakin ne domin tabbatar da gaskiya a aikace da sauran tsare-tsare na aikin hajjin.
Aderibigbe, wanda ma’aikatar sa ke sa ido a kan Hukumar Alhazai ta Jihar, ya kara da ba da tabbacin cewa, shirin zai tabbatar da bin diddigin al’amuran alhazai da aikace-aikacen alhazai a jihar.
Daga nan sai ya umurci alhazai musulmi da su shiga shafin yanar gizo mai suna muslimpilgrim.osunstate.gov.ng don yin ragistar Hajjin 2025, yayin da aka ce Kiristoci mahajjata su nemi a christianpilgrim.osunstate.gov.
A kokarin tabbatar da sauki, tare da Tsantsaini da, gaskiya da kuma samun damar yin rajistar aikin Hajji l gwamnatin jihar Osun karkashin jagorancin Gwamna Ademola Jackson Nurudeen Adeleke ta kaddamar da shafukan Musulmi da Kirista ga duk mai niyyar zuwa Hajji zasu yi ragistar.
Alhazan Musulmi da Kirista a Jihar Osun na shekarar 2025 mai tsarki.“Tsarin da aka amince da shi zai tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin ayyukan Hajji da masu zuwa Kudus, tare da tabbatar da cewa shirin zai tabbatar da gaskiya da rikon amana ga aikin Hajji, .“Saboda wannan ci gaba, gwamnatin jihar Osun tana rokon jama’a masu sha’awar zuwa aikin hajjin shekarar 2025 da su shiga Muslim pilgrim.osunstate.gov.ng domin neman gurbin hajjin 2025. Yayin da su kuma Kiristoci zasu shiga Mahajjata su nemi a christianpilgrim.osunstate.gov.ng.”
Jaridar Punch