Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta bayyana cikakken shirinta ne yayin da ta fara aikin samar Bizar aikin Hajjin 2025 a hukumance.
Da yake jawabi bayan wani taron gudanarwa a ofishinsa, Darakta Janar na Hukumar, Lamin Rabi’u Danbappa, ya tabbatar da cewa an samar da dukkan shirye-shiryen da suka dace don saukaka tsarin neman Biza ga maniyyata.
Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Sanar Da Ranar Karshe Ta Ajiye Kudin Aikin Hajin 2025
Ya jaddada cewa sanya maniyyatan cikin tsarin rukuni-rukuni, wani muhimmin al’amari ne mai muhummanci na hukumar, wanda zai ci gaba kamar yadda aka yi a shekarun baya don tabbatar da inganta aiki.
A wani labarin kuma, Daraktan ayyukan Hajji na hukumar, Muhammad Ghali Muhd, ya bukaci dukkan maniyyatan da har yanzu ba su mika fasfo dinsu ba, da su gaggauta yin hakan domin kaucewa tsaiko.
Ya kuma ba da tabbacin hukumar tare da hadin gwiwar jami’an alhazai na kananan hukumomi, za su bi ka’idojin kasar Saudiyya sosai wajen shirya mahajjatan.
Hukumar ta jaddada kudirinta na ganin cewa duk wani mahajjaci da ya yi rajista ya kammala aikin ba tare da wata matsala ba.