Hukumar wayar da kan al’uma ta kasa NOA, ta jaddada aniyarta na tallafawa hukumar jin dadin alhazai ta Bauchi a fannin ilmantar da Alhazai tare da fadakar dasu.
A sanarwar da Jami’in yada labarai na hukumar, Muhammad Sani Yunusa ya sanyawa hannu, yace Sabuwar Daraktar hukumar ta NOA ta jihar Bauchi Mrs. Theresa Omega ta bayyana haka a lokacin da ta jagoranci tawagar hukumar ta da suka kai ziyarar fahimtar juna a hukumar domin gabatar da sabon Darakta NOA.
Misis Theresa ta bayyana cewa hukumarta na da alhakin sadar da manufofin gwamnati da shirye-shiryen gwamnati da kuma inganta kishin kasa, inda ta jaddada cewa za su ci gaba da kara wayar da kan alhazai kan yadda za su rungumi canjin halaye a lokacin aikin hajji.
Da take yaba dangantakar hukumar, ta kara da cewa hukumar za ta nuna fiye da yadda ake samu ta fuskar hadin gwiwa da hukumar domin cimma burin da ake son cimma
Da yake mayar da jawabin, Sakataren zartarwa na Hukumar, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ya taya Sabuwar Daraktan NOA na jiha a jihar Bauchi murna.
Ya ce hukumar ta NOA na hada kai da hukumar ta fannin ilimi da wayar da kan jama’a, inda ya bayyana hukumomin biyu a matsayin abokan hadin gwiwa.
Imam Abdurrahman yayin da yake ba da tabbacin ci gaba da yin hadin gwiwa da Hukumar ta NOA, ya bukaci su ci gaba da ba su goyon baya a duk lokacin gudanar da aikin hajji.