Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta sanar da tsaurara matakan kiwon lafiya ga maniyyatan da ke shirin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025, inda ta jaddada cewa masu lafiya ne kadai ya kamata su yi aikin hajji.
Da take ambaton matsanancin wahalar aikin Hajji – inda mahalarta za su iya yin tafiya har zuwa kilomita 25 a kowace rana a ƙarƙashin tsananin zafin bazara – ma’aikatar ta yi gargadin cewa waɗanda ke da yanayin kiwon lafiya ya kamata su sake yin la’akari da halartar, a cewar wani labarin Khaleej Times da aka buga ranar Lahadi.
Mutane fiye da 65, waɗanda ke da cututtuka na yau da kullum irin su cututtukan zuciya, matsalolin koda, matsalolin numfashi ko ciwon sukari, da kuma wadanda ke da raunin rigakafi (ko dai na haihuwa ko samu), masu ciwon daji, mutanen da ke da cututtuka dake kisa, mata masu ciki da yara yan kasa da shekara 12. da su dage aikin hajjinsu.
Shawarar ta nuna ƙarin haɗarin matsalolin lafiya waɗanda waɗannan ƙungiyoyi masu rauni za su iya fuskanta a cikin mawuyacin yanayi na aikin hajji. Sama da mahajjata 1,300 ne rahotanni suka ce sun mutu a aikin Hajjin 2024, sakamakon tsananin zafi da ya mamaye fadin kasar Saudiyya da kuma birnin Makkah.
An danganta mutuwar da “tafiya mai nisa karkashin hasken rana kai tsaye ba tare da isasshen matsuguni ko kwanciyar hankali ba.” Wadanda suka mutu sun kuma hada da tsofaffi da kuma masu fama da rashin lafiya.
Tsananin zafin da ya kai 51.8 ℃, ya afkawa mutane kusan miliyan biyu da suka yi tururuwa zuwa Makkah domin gudanar da aikin Hajjin na 2024
Source: Dhaka Tribune