A madadin Jaridar Hajj Chronicles, muna mika sakon taya murna ga, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, bisa cika kwanaki 100 a kan kujerar shugabancin hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON).
Wa’adin shugabancinka ya riga ya nuna kwazonka na kirkire-kirkire, hadin gwiwa, da kuma bayyana gaskiya a ayyukan Hajji da Umrah.
Tun daga shigar da masu ruwa da tsaki a duk fadin kasar zuwa fara gyare-gyare bisa dabaru, shugabancinka na kafa sabon ma’auni na inganci da hada kai wajen gudanar da ayyuka.
Mun aminta da hazaka da hangen nesanka na ganin anyi aikin Hajji mai cike da inganci ga alhazan Najeriya da sadaukarwar da ka yi na biyan bukatunsu cikin gaskiya da tausayi.
Yayin da kake murnar wannan nasara, Jaridar Hajj Chronicles za ci gaba da jajircewa wajen tallafawa ayyukan NAHCON ta hanyar bayar da rahoton ayyukan ku, nasarori da kuma tasirin da kuka samu a fannin aikin Hajji.
Da fatan wannan jagoranci naka a wannan matsayi mai daraja zai ci gaba da samar da manyan nasarori domin amfanin alhazan Najeriya da sauran al’ummar musulmi baki daya.
Salamu alaikum,
Daga Hajj Chronicles
Bunkasa Rahotannin Ayyukan Haji