Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Gombe ta kaddamar da aikin gwajin lafiya ga maniyyatan Hajjin 2026, a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da cewa dukkan maniyyatan jihar suna cikin koshin lafiya domin gudanar da ibadun Hajji masu bukatar ƙarfi da juriya a Ƙasar Saudiyya.
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da shirin, Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Sa’adu Hassan, ya bayyana cewa gwajin lafiyar wajibi ne bisa umarnin hukumomin Saudiyya, inda ya jaddada cewa dole ne duk maniyyata su bi ka’idojin ba tare da wani rangwame ba.
A cewarsa, wannan tsari na daga cikin matakan lafiya da tsaro na ƙasa da ƙasa da aka kafa domin kare rayukan alhazai da kuma tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin sauƙi.
Ya kara da cewa ibadun Hajji na bukatar ƙarfi da juriya sosai, don haka lafiyar jiki na da matuƙar muhimmanci.
Alhaji Sa’adu Hassan ya bayyana cewa duk maniyyacin da aka gano yana da babbar matsalar lafiya ba za a bari ya je Hajjin 2026 ba. Ya ce ko da yake wannan mataki yana da wahala, amma wajibi ne domin kauce wa matsalolin gaggawa na lafiya da kuma kare jin daɗin maniyyata.
Ya kuma bayyana cewa ba za a yarda mata masu juna biyu su je Hajjin 2026 ba, sakamakon barazanar lafiya ga uwa da jaririn cikinta, la’akari da tsananin wahalhalun ibadun Hajji da kuma yanayin zafin ƙasar Saudiyya.
Sakataren Zartarwar ya ce za a gudanar da gwajin lafiyar ne kashi-kashi domin tabbatar da cikakken tsari da gaskiya. Ya bayyana cewa an fara zagaye na farko a halin yanzu, yayin da za a gudanar da zagaye na biyu bayan watan Ramadan.
Ya ce zagaye na biyu yana da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da cewa babu wata mai juna biyu da za ta tafi aikin Hajji, hakan zai hana matsalolin lafiya na gaggawa a minti na ƙarshe tare da tabbatar da bin dokokin Hajjin Saudiyya gaba ɗaya.
Sa’adu Hassan ya yi kira ga duk maniyyata da su ba da cikakken haɗin kai ga jami’an lafiya tare da bayar da sahihin bayani kan lafiyarsu, yana mai gargaɗin cewa ɓoye matsalar lafiya na iya kaiwa ga hana mutum zuwa aikin Hajji.
Ya sake jaddada kudurin Gwamnatin Jihar Gombe da Hukumar Jin Daɗin Alhazai na tabbatar da tsaro, walwala da jin daɗin maniyyata, yana mai tabbatar da cewa Hukumar za ta gudanar da Hajjin 2026 cikin nasara ba tare da wata tangarda ba.
A nasa jawabin, Babban Daraktan Asibitin Kwararru na Gombe, Dakta Sambo Dawa, ya tabbatarwa maniyyata cewa an tanadi dukkan abubuwan da suka dace domin gudanar da gwajin lafiyar cikin sauƙi da inganci.
Dakta Dawa ya ce an tura kwararrun jami’an lafiya da suka hada da likitoci, ma’aikatan jinya da sauran ma’aikatan lafiya domin gudanar da gwajin, domin tabbatar da cewa an duba kowane maniyyaci yadda ya kamata.
Ya kara da cewa an samar da kayayyakin aikin lafiya na zamani da dakunan gwaji domin taimakawa wajen yin sahihin bincike da tantance lafiyar maniyyata, yana mai jaddada kudurin asibitin na kiyaye mafi girman matakan aikin lafiya a duk tsawon shirin.
Babban Daraktan ya tabbatar wa maniyyata cewa za a gudanar da gwajin cikin adalci, sirri da girmama mutuncin dan Adam, yana mai cewa manufar shirin ba hana kowa yin Hajji ba ce, sai dai tabbatar da tsaro da shiri na gari.
Ya bukaci maniyyata da su dauki gwajin lafiyar a matsayin matakin kariya da rigakafi, yana mai cewa gano matsalar lafiya da wuri na iya ba da damar samun magani cikin lokaci tare da kara yiwuwar halartar Hajji a nan gaba.
Dakta Dawa ya kuma jaddada muhimmancin kula da lafiya tun kafin tafiya, yana mai kira ga maniyyata da su bi dukkan shawarwari da umarnin likitoci da za a ba su yayin gwajin.
Wasu daga cikin maniyyatan da suka halarci gwajin sun yabawa Hukumar da Gwamnatin Jihar Gombe bisa fifita lafiyarsu da tsaronsu, suna masu bayyana shirin a matsayin wanda ya zo a kan lokaci kuma ya zama dole.
Wasu kuma sun yi kira da a rika ci gaba da wayar da kan maniyyata kan kula da lafiya, musamman wajen sarrafa cututtuka masu tsanani da kuma kiyaye lafiyar jiki kafin tafiya Hajji.
Gaba ɗaya, fara aikin gwajin lafiyar maniyyata ya zama wani muhimmin mataki a shirye-shiryen Hajjin 2026. Tare da tsauraran matakan lafiya, goyon bayan kwararrun jami’an lafiya da kuma jajircewar hukumomi, Jihar Gombe na fatan tabbatar da Hajji mai tsaro, nasara da cikar ruhi ga dukkan maniyyatan da suka cancanta.

