Daga Ahmad Muaz Hukumar Aikin Hajj ta Kasa (NAHCON) ta kammala tantance wuraren kwana da dakunan dafa abinci a Madinah a matsayin wani bangare na shirin farko na aikin Hajjin 2026.
An gudanar da aikin tantancewar ne daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Nuwamba 2025, kuma Farfesa Abubakar A. Yagawal, Kwamishinan dake kula da Tsare-tsare, Bincike, Kididdiga da sauransu ne ya jagoranci aikin.
Tawagar ta kunshi wakilan Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, da na hukumar da kuma na kungiyar Shugabannin Hukumomin Alhazai na Jihohi, tare da manyan jami’an gudanarwa na Hukumar.
Babban aikin tantancewar shi ne auna yanayin shiri na duk masu samar da ayyukan.
Tawagar ta gudanar da bincike kan otal-otal, tabbatar da ingancin takardun aiki, da tabbatar da bin ka’idojin Saudiyya da kuma na NAHCON game da masauki da abinci.
A cikin kwanaki uku, tawagar ta duba otal-otal sama da 20 a yankin Markaziyya da wuraren dafa abinci 7.
Binciken ya nuna cewa an bi ka’idojin masauki da abinci sosai, tare da ba da muhimmanci kan aminci da tsafta.
Lokacin kaddamar da kwamitin a Makkah kafin tafiyarsu, Shugaban Hukumar kuma Babban Jami’in Gudanarwa na NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya umurci mambobin da su kiyaye mafi girman da’a da kwarewa a yayin gudanar da aikin su.
“Amincewa, rashin son kai, da nuna gaskiya dole ne su jagoranci kowane bangare na wannan binciken. Ku gudanar da ayyukanku da himma da horo na kwararru. Jin dadin, aminci, da kwanciyar hankali na alhazan Nijeriya ya kasance babban fifikonmu, kuma duk sakamakon binciken dole ne ya nuna wannan jajircewar,” in ji Shugaban.
Farfesa Usman ya sake tabbatar da kudirin NAHCON na karfafa tsarin sa ido, inganta rikon amana tsakanin masu samar da hidima, da tabbatar da cewa alhazan Nijeriya sun samu kulawa daidai da abinda suka biya.
Ana sa ran tawagar tantancewar za ta mika cikakken rahotonta ga kwamitin gudanarwar Hukumar domin yin nazari da daukar matakin siyasa.

