Bayan shawarwari da dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabannin hukumomin Alhazai na jihohi da samun amincewar Gwamnatin Tarayya, Shugaba NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya sanar da farashin Hajj na 2026 kamar haka:
Yankin Maiduguri Yola (Jihohin Yobe, Borno, Adamawa da Taraba) za su biya: N8,118,333.67
Sauran Jihohin Arewa za su biya: N8,244,813.67
Jihohin Kudu za su biya: N8,561,013.67
Idan aka kwatanta da abin da aka biya a bara, a bana kowanne ɗan Alhaji zai biya kusan naira dubu dari biyu (₦200,000) ƙasa da na bara.
A halin yanzu, tawagar NAHCON da ke Saudiyya sun gana kuma sun rattaba hannu kan yarjejeniya da Kamfanin Bayar da Hidimar Hajj na shekarar 2026 (Mashareeq Al-Zahabiyya) da kuma Kamfanin Sufuri (Daleel Al-Ma’aleem).
Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi, ya yi kira ga dukkan masu niyyar yin Hajj da su kammala biyan kuɗin su kafin ranar 31 ga Disamba, 2025.