Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Sokoto, Alhaji Aliyu Musa, ya isa Ƙasar Saudiyya domin tabbatar da kammala ingantattun shirye-shirye don samun nasarar gudanar da aikin Hajjin 2026 ga alhazan jihar.
KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN; Hukumar Alhazzai ta Sokoto ta samu nasarar sanya Bayanan Mahajjatan 2,404 a Manhajar E-Track Masar
A sanarwar da Shugaban sashen yada labarai da sadarwa na hukumar, Faruku Umar ya fitar, yace ziyarar na daga cikin matakan da hukumar ke ɗauka tun da wuri domin tabbatar da jin daɗi, walwala da tsaron dukkanin maniyyata daga jihar a lokacin aikin Hajji mai zuwa.
Domin ƙara ƙarfafa shirye-shiryen, ana sa ran Babban Sakatare na hukumar, Alhaji Ibrahim Umar JJ, zai bi sahun shugaban domin gudanar da cikakken bincike kan masauki da kuma tsarin ciyarwa da aka tanadar wa alhazan Jihar Sokoto a Makkah.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Sokoto na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da gudanar da Hajji cikin sauƙi da kwanciyar hankali tare da cika manufofin ibada ga dukkanin alhazai, ta hanyar tsare-tsare masu inganci da kuma tantance dukkan muhimman ayyuka a fili.

