Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya sanar da hakan a ganawarsa da manema labarai a Dutse.
Labari Makamancin Wannan: Hajin 2025: Hukumar Alhazai ta Jigawa ta mika fiye da naira miliyan 4,000 na kudin Alhazai ga hukumar NAHCON
Labbo ya ce har yanzu wadanda suka yi ajiyar kudadensu su na kokarin cika kudadensu na aikin hajji
A sanarwar da Jami’in Hulda Da Jama’a na Hukumar, Habibu Yusuf Babura ya sanyawa hannu, Alhaji Ahmed Umar Labbo yana mai cewar hukumar ta biya hukumar aikin hajji ta kasa kudi naira miliyan dubu takwas a matsayin kudaden dawainiyar maniyatan aikin hajjin bana na jihar Jigawa.
Darakta Janar na hukumar alhazan ta jihar Jigawan yana mai cewar kamfanin Max air ne zai yi jigilar maniyatan jihar Jigawa zuwa kasa mai tsarki a bana.
Ya kuma ce hukumar ta kammala duk wani shiri na jigilar maniyatan zuwa kasa mai tsarki da suka hadar da samar musu da masauki a kusa da harami da samar da jakankuna da kuma uniform.
A cewarsa tuni an fara bizar maniyatan aikin hajjin bana rukuni rukuni yayinda aka dawo da aikin bitar maniyata na rana rana domin baiwa maniyatan damar samun ilmin gudanar da aikin hajjin bana.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kuma yabawa gwamna Umar Namadi bisa kulawar sa ga aiyukan hukumar.