Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai na Jihar Gombe, Alhaji Sa’ad Hassan, ya kaddamar da aikin rigakafi ga alhazan da ke shirin zuwa Hajji a yau a Sansanin Koyar da Hajj na Gombe.
KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN : Hukumar Alhazai ta Gombe Ta Fara Rabon Jaka da Tufafi Ga Mahajjatan 2025
A jawabinsa yayin taron kaddamarwar, Alhaji Sa’ad Hassan ya jaddada cewa yin rigakafi dole ne ga dukkan alhazan da suka yi rajista karkashin Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Gombe. Ya bayyana cewa wannan aikin yana da matuƙar muhimmanci wajen shirin Hajjin bana domin kare lafiyar alhazan yayin gudanar da ibadarsu a kasa mai tsarki.
Ya kuma sanar da cewa kowanne alhaji daga jihar Gombe zai karɓi dala 500 a hannu a matsayin Kuɗin Tafiya (BTA). Ya tabbatar da cewa dukkan shirye-shiryen da suka kamata an kammala su domin tabbatar da cewa kowane alhaji ya karɓi kuɗinsa.
Alhaji Sa’ad Hassan ya bayyana cewa adadin alhazan da ke shirin tafiya Hajjin 2025 daga jihar Gombe ya kai 962. Ya nuna godiya ga Gwamnatin Jihar Gombe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa ci gaba da tallafa wa hukumar, yana mai bayyana cewa gwamnatin jihar ta biya harajin Hajji gaba ɗaya a madadin alhazan jihar.
Sakataren Zartarwa ya ƙara bayyana cewa aikin rigakafin zai kasance ne kawai ga alhazan da suka biya kuɗinsu ta Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Gombe ko ta Bankin Jaiz. Ya jaddada cewa waɗanda suka biya kuɗinsu ta wasu hukumomi masu zaman kansu ba su cancanci yin rigakafin da hukumar ke bayarwa ba.
Alhaji Sa’ad Hassan ya sake nanata muhimmancin bin ƙa’ida da doka, yana mai bayyana cewa hukumar ta himmatu wajen tabbatar da cewa dukkan alhazan da suka yi rajista sun cika dukkan sharuddan kiwon lafiya da ake buƙata kafin tafiyarsu zuwa ƙasa mai tsarki.
A karshe ya shawarci dukkan alhazai da su kasance masu bin doka da oda a lokacin zamansu a ƙasar Saudiyya. Ya tunatar da su cewa ɗabi’a ta gari na da matuƙar muhimmanci wajen nasarar ibadar su da kuma kar martabar jihar Gombe da Najeriya gaba ɗaya a idon duniya.
Bikin kaddamar da rigakafin ya samu halartar jami’an hukumar alhazai, shugabannin addini da kuma sauran manyan masu ruwa da tsaki.
Aikin yin rigakafin na nuna irin matakin shirin da jihar Gombe ta kai domin Hajjin 2025, yana kuma bayyana cikakken jajircewar gwamnatin jihar wajen kare lafiyar alhazanta da tabbatar da walwalarsu.
Gombe