Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Sokoto (PWA) ta halarci taron haɗin gwiwar shirye-shiryen aikin Hajji wanda Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta shirya tare da shugabannin Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na jihohi.
A sanarwar da Shugaban sashen yada labarai da sadarwa na Hukumar, Faruku Umar ya sanyawa hannu, yace an gudanar da taron mai matuƙar muhimmanci a Dakin Taro na NAHCON da ke Ummul Judd, Makkah, ta kasar Saudiyya, a matsayin wani ɓangare na ci gaba da shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2026.
Tawagar Jihar Sokoto ta samu jagorancin Shugaban Hukumar, Alhaji Aliyu Musa, tare da Daraktan Mulki Alhaji Ladan Ibrahim.
Muhimman batutuwan da aka tattauna a taron sun haɗa da sabbin bayanai kan hulɗa da hukumomin Saudiyya, tsare-tsaren jigilar maniyyata ta jiragen sama da haɗin gwiwa da kamfanonin jiragen da aka zaɓa, shirye-shiryen masauki, samar da abinci, da kuma shirye-shiryen lafiya da yaɗa labarai gabanin aikin Hajji mai zuwa.
Haka kuma, taron ya bayar da cikakken bayani kan shirye-shiryen Hajjin 2026, inda aka mayar da hankali kan matakin shirin da jihohi suke akai, sarrafa bayanan maniyyata, da kuma hanyoyin takardun izini shiga kasa domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin sauƙi ba tare da wata matsala ba.
Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ne ya jagoranci taron, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai da yin shiri tun da wuri a tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki domin samun nasarar aikin Hajji.
Halartar Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Sokoto a taron na nuna ƙudurin Hukumar na tabbatar da ingantaccen tsari, haɗin gwiwa, da jin daɗin maniyyatan jihar a lokacin aikin Hajjin 2026.

