Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shiri na musamman a gidan rediyo domin taimaka wa maniyyata wajen kammala karatun horon Hajji a cikin watan Ramadan mai alfarma.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi, ya sanya wa hannu, ya ce Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayyana hakan a wajen rufe Bitar Alhazai ta mako-mako da aka gudanar a Makarantar Nazarin Larabci ta Kano.
Darakta Janar ɗin ya bayyana cewa manufar wannan shiri ita ce sauƙaƙa ilimin Hajji ga maniyyata ta hanyar ba su damar sauraron darussan horo daga gidajensu ta kafafen rediyo da aka ware musamman a cikin watan Ramadan.
Ya ƙara da cewa shirin zai ƙunshi cikakken bayani kan yadda ake gudanar da ibadun Hajji, hanyoyin tafiya, sharuddan lafiya, da kuma shirye-shiryen ruhaniya domin tabbatar da cewa dukkan maniyyata sun samu isasshen bayani da shiri kafin tafiya.
Alhaji Abubakar Matawalle ya tabbatar wa jama’a da cewa Hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da tafiya mai sauƙi daga Kano har zuwa ƙasa mai tsarki, tare da samar da kulawa da jin daɗin alhazai.
Ya jaddada cewa Hukumar za ta ci gaba da bayar da cikakken horo, shiriya da kulawa domin tabbatar da samun nasarar gudanar da Hajji cikin kwanciyar hankali da cika alkawarin ibada ga daukacin alhazan Jihar Kano.
Hukumar ta kuma ƙarfafa wa dukkan maniyyata gwiwa da su rika sauraron shirin rediyon domin ƙara fahimtar yadda ake gudanar da ibadun Hajji a wannan wata mai albarka na Ramadan.

