Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta ƙara kaimi wajen ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin jiragen sama da tsaro da tabbatar da gudanar da aikin jigilar maniyyata cikin tsari da kwanciyar hankali.
Kamar yadda Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya bayyana, Hukumar ta bayyana aniyarta ta zurfafa alaƙa da Federal Airports Authority of Nigeria (FAAN) da kuma Nigeria Customs Service.
Daraktan Janar na Hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar girmamawa da ya kai wa manyan jami’an hukumomin a Kano.
A yayin ziyararsa ga Manajan shiyya na FAAN a Malam Aminu Kano International Airport, Matawalle ya ce Hukumar na da niyyar ƙarfafa kyakkyawar alaƙa musamman a fannin tsaro da inganta ayyukan da suka shafi jigilar maniyyata zuwa ƙasa mai tsarki.
Ya jaddada cewa haɗin kai mai ƙarfi tsakanin Hukumar Jin Daɗin Alhazai da mahukuntan filin jirgin sama na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da tafiyar maniyyata cikin sauƙi ba tare da tangarda ba.
Da yake mayar da jawabi. Manajan shiyya na filin jirgin sama, Alhaji Musa Okikiri, ya yaba da ziyarar tare da bayyana ta a matsayin mai muhimmanci a wannan lokaci.
Ya kuma sanar da cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da cikakken gyaran tashar alhazai ta filin jirgin domin inganta kayayyakin aiki da hidimomin da ake bayarwa kafin jigilar maniyyatan bana.
Haka zalika, Daraktan Janar ya kai ziyarar girmamawa ga Rundunar Kano/Jigawa ta Hukumar Kwastam domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tantancewa da binciken kayayyakin maniyyata.
Matawalle ya jaddada buƙatar wayar da kan maniyyata musamman kan abubuwan da aka haramta ko kayayyakin da ba a yarda da su ba, domin kauce wa jinkiri yayin tashi. Ya kuma roƙi Hukumar Kwastam da ta mara wa shirye-shiryen wayar da kai baya, ciki har da shiga shirye-shiryen rediyo domin ilmantar da maniyyata.
A nasa jawabin, Mataimakin Kwanturola mai kula da Harkokin Gudanarwa, Mista S.S. Shehu, ya tabbatar da shirye-shiryen Rundunar na bayar da cikakken haɗin kai. Ya ce za su yi aiki kafada da kafada da Hukumar domin rage jinkiri yayin tantancewa tare da kiyaye dokoki da ƙa’idoji.
A cewar masu lura da al’amura, ziyarar na nuna ƙudurin Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano na ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomi daban-daban domin samar da ingantaccen, tsaro da kuma nasarar gudanar da aikin Hajji ga al’ummar Jihar Kano.

