Biyo bayan umarnin Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) kan kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026, Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da cewa an amince da kuɗin Hajj naira Miliyan Takwas, Dubu Dari Biyu da Arba’in da Hudu, Dari Takwas da Goma Sha Uku, Kobo Sittin da Bakwai (₦8,244,813.67).
A sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na Hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya fitar, yace Daraktan Janar na Hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya tabbatar da cewa wannan kuɗi ya shafi dukkan masu niyyar zuwa aikin Hajji daga jihar Kano.
Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana cewa, waɗanda suka riga suka biya naira miliyan 8.5 za a mayar musu da ₦255,186.33 idan suka gabatar da rubutacciyar buƙatar yin hakan ga hukumar.
Ya ƙara da cewa, masu niyyar biyan kuɗi za su biya cikakken adadin kuɗin Hajji wato ₦8,244,813.67.
Haka kuma ya sanar da cewa ranar ƙarshe ta biyan kuɗin ita ce 31 ga Disamba, 2025, kamar yadda NAHCON ta umarta.
Daraktan Janar ya yi kira ga dukkan masu niyyar zuwa aikin Hajji su tabbatar sun kammala biyan kuɗinsu kafin ranar ƙarshe domin tabbatar da samun gurbin tafiya.