Hukumar Jin Dadi ta Alhazai ta Jihar Kano ta bayyana shirinta na ƙara haɗa kai da Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) domin inganta ayyuka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano International Airport.
A sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na Hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya fitar, yace Shugaban Hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, wanda Daraktan Harkokin Hajji, Alhaji Muhammad Ghali Muhammad, ya wakilta, ya bayyana haka yayin ziyarar ban girma ga Manajan Yanki na filin jirgin a yau.
Ya ce Hukumar za ta ci gaba da jajircewar da ta nuna a lokacin aikin Hajjin da ya gabata, tare da shirin bayar da gudummawa wajen gyaran masallacin da ke cikin sashen kashe gobara na filin jirgin.
Alhaji Ghali ya kuma tabbatar da cewa Hukumar za ta kasance tana bayar da cikakken goyon baya don tabbatar da gudanar da ayyukan filin cikin sauƙi da nasara, musamman a lokacin aikin Hajji.
A nasa jawabin, Manajan shirya na filin jirgin Malam Aminu Kano, Alhaji Ahmadu Danjuma, ya jinjinawa Hukumar Alhazai ta Kano bisa wannan gudummawa da goyon baya.
Ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince za a kammala gyaran bangaren tashin Alhazai (Hajj Terminal) kafin a fara jigilar Alhazan bana.
Haka kuma, Alhaji Danjuma ya yabawa Hukumar Alhazai ta Kano bisa bin ka’idoji da dokoki yadda ya kamata a lokacin aikin Hajjin da ya gabata.