Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Sokoto ta samu nasarar kammala sanya bayanan dukkanin mahajjata 2,404 da suka yi rajista daga jihar a manhajar E-Track Masar, kafin rufe manhajar a hukumance da hukumomin ƙasar Saudiyya suka yi.
A sanarwar da Shugaban sashen yada labarai da sadarwa na Hukumar, Faruku Umar ya sanyawa hannu, yace Shugaban Hukumar, Alhaji Aliyu Musa, ne ya bayyana hakan a yau yayin wata ganawa da Mataimakan Jami’an Rajistar Hajji daga ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Alhaji Aliyu Musa ya bayyana cewa, da rufe manhajar Masar, an shiga sabon mataki na gudanar da aikin Hajji, inda ya nuna cewa hukumomin Saudiyya tare da haɗin gwiwar Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), sun bullo da sabbin tsare-tsare domin tabbatar da gudanar da aikin Hajjin 2026 cikin sauƙi da tsari mai kyau.
A cewarsa, ɗaya daga cikin muhimman sabbin ƙa’idojin da aka shimfiɗa wa kamfanonin jiragen sama shi ne bayar da tikitin tafiya tun kafin ranar tashi, inda kowane mahajjaci zai san takamaiman ranar tafiyarsa, lokaci da kuma wurin tashi.
Ya yi gargaɗin cewa rashin halartar jirgi a ranar da aka tsara (no-show) zai jawo hukunci, domin za a haɗa tikitin kowane mahajjaci ta hanyar dijital da Katin Nusuk ɗinsa.
Shugaban ya ƙara da cewa, daga yanzu mahajjata za su yi tafiya ne a rukuni-rukuni na mutane 45, inda kowane rukuni zai tashi tare, a sauke su tare a otal-otal ɗaya a Makkah, Madinah da Masha’ir, sannan su dawo Nijeriya tare bayan kammala aikin Hajji.
Haka kuma ya bayyana cewa sabon tsarin ya tanadi cewa NAHCON za ta tura bayanan mahajjata kafin isowarsu (pre-arrival data) a manhajar Nusuk Masar akalla sa’o’i 72 kafin tashin kowanne jirgin da zai ɗauki mahajjata zuwa Ƙasar Saudiyya.
Ya jaddada cewa ba za a amince da sauya rukuni ba bayan an fitar da biza.
Alhaji Aliyu Musa ya tabbatar da cewa Hukumar ta daidaita tsarin rajistarta domin bin dukkan sabbin ƙa’idojin, tare da manufar kare jin daɗin mahajjatan Jihar Sokoto da kuma tabbatar da gudanar da aikin Hajji ba tare da wata tangarɗa ba.

