Daga Abdulkadir Aliyu Shehu
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Musulmai ta Jihar Gombe ta fara raba jakunkuna da Tufafi ga dukkan mahajjatan da ke shirin zuwa aikin Hajjin shekarar 2025, yayin da shirye-shiryen tafiya suka yi nisa. Babban Sakataren hukumar, Alhaji Sa’ad Hassan, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a shelkwatar hukumar da ke Gombe.
Karanta makamancin labarin: Gombe Pilgrims Board Wraps Up BITA Mid-Term Break, Prepares for Ramadan
Alhaji Hassan ya bayyana cewa mahajjata 962 daga jihar Gombe ne suka kammala dukkanin matakan rajistar da ake buƙata domin aikin hajjin bana. Ya tabbatar da cewa an riga an tanadi kuɗin tafiya na wato (BTA) ga kowane mahajjaci.
Haka zalika, ya sanar da isowar rigakafi da kuma katunan wato (Yellow Card), inda ya ce za a fara aikin rigakafin mako mai zuwa a wuraren da aka ware a fadin jihar.
A wani muhimmin bayani, Alhaji Hassan ya bayyana cewa an dage ranar fara jigilar mahajjatan jihar Gombe zuwa kasa Mai tsarki daga ranar 13 ga watan Mayu zuwa 20 ga watan Mayu. Ya ce wannan canjin ya biyo bayan shirye-shiryen ƙarshe na tabbatar da ingantaccen tsari da sauƙin jigila.
“Tashar jirgin sama ta Zakariya Maimalari da ke Gombe tana dab da kammala shirye-shiryen jigilar mahajjata gaba ɗaya. Jami’an hukumar za su gana da hukumomin filin jirgin domin kammala shirin tashi,” in ji shi.
Alhaji Hassan ya tabbatar wa mahajjatan da ke shirin tafiya cewa an tanadi masaukai masu kyau a wuraren ibada na ƙasa mai tsarki — ciki har da Mina, Arafat da Muzdalifah. Ya kuma bayyana cewa an shirya abinci mai gina jiki da ya dace da al’adun mahajjata domin jin daɗinsu yayin gudanar da ibada.
Babban Sakataren ya yi gargaɗi mai ƙarfi ga mahajjata da kada su bayar da tufafin su da aka basu ga wasu yayin da suke cikin Makkah da Madinah, yana mai bayyana cewa hakan na iya jawo barazanar tsaro da kuma janyo matsaloli a aikin hajjin.
Ya ƙara jaddada cewa hukumar ba za ta amince da tafiyar mata masu juna biyu, tsofaffi da kuma waɗanda ke fama da matsanancin ciwon ba, saboda dalilai na kiwon lafiya.
A ƙarshe, Alhaji Hassan ya bukaci mahajjata su bi doka da ƙa’idodin da hukumar da kuma hukumomin Saudiyya suka shimfiɗa, domin samun hajji mai cike da nutsuwa da albarka.