Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta mayarwa alhazan jihar Kebbi 4,936 kudaden da suka kai sama da Naira miliyan 301.56 da suka yi aikin hajjin shekarar 2023.
A sanarwar da mai bawa gwamnan jahar shawara na musammam kan Harkokin Yada Labarai Yahaya Sarki ya sanyawa hannu, tace kowanne daga cikin mahajjata 4,936 da suka halarci aikin Hajjin shekarar 2023 za a mayar musu da kudi Naira 61,080.
Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kebbi, Alhaji Faruku Aliyu Yaro Enabo (Jagaban Gwandu) ne ya bayyana hakan a yayin wani taro da aka gudanar domin tattauna batun mayar da kudaden da Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta fitar.
Ya ce tuni aka saka kudaden a hannun hukumar domin rabawa wadanda suka da hakki. Ana mayar da kudaden ne bisa bin umarnin NAHCON na biyan diyya ga maniyyata bisa ayyukan da ba a yi ba a lokacin aikin Hajjin 2023.
Ya ce, “Bayan na karbi kudaden daga NAHCON, na sanar da Gwamna, wanda ya umarce ni da in fara shirin mayar da kudaden ga maniyyata, tare da shugabannin kananan hukumomi 21 da suka shaida kuma sun tabbatar da yadda lamarin ya gudana.
Enabo ya bukaci shuwagabannin majalisun kananan hukumomin da su kuma sanya ido a kan aikin domin tabbatar da cewa dukkan maniyyatan da abin ya shafa sun samu kudadensu.
Ya kuma bayyana cewa hukumar EFCC, ICPC, NSCDC, ‘yan sanda, DSS da sauran jami’an tsaro masu alaka da wannan aikin za su sa ido sosai.
Alhaji Faruku ya bayyana cewa hakki ne da ya rataya a wuyan hukumar ta tabbatar da cewa dukkan maniyyatan da suka cancanta sun samu kudadensu ba tare da bata lokaci ba.
Ya kuma jaddada cewa adadin maniyyatan da abin ya shafa a jihar Kebbi sun kai 4,936 wanda kowannen su zai samu Naira 61,080. Taron ya samu halartar shuwagabannin kananan hukumomi, shugabannin hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kebbi, da jami’an alhazai da daraktoci na hukumar.
Bugu da kari, Alhaji Faruku ya bukaci maniyyata aikin hajjin 2025 mai zuwa da su gaggauta biyan kudadensu. Ya kuma kara da cewa NAHCON ta kara wa’adin biyan kudi har zuwa karshen watan Disamba na shekarar 2024, tare da karfafa biyan kudi da wuri domin samar da ingantattun masauki, jigilar kayayyaki, da sauran muhimman ayyuka a lokacin aikin Hajji.