Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta gayyaci dukkanin kamfanonin jirgin yawo da ke da lasisi don gudanar da taron karawa juna sani a gobe 2 ga watan Oktoba domin tattaunawa kan aikin Hajjin 2025.
Taron wanda aka shirya gudanarwa ta hanyar Manhajar Zoom, za a fara gudanar da shi da karfe 11 na safe a gobe Laraba
Jaridar (Hajj Reporters) ta rawaito cewa wata majiya dake da kusanci da ita, ta bayyana musu cewa an turawa dukkanin kamfanonin hanyar da zasu shiga taron ga dukkanin Kamfanonin Jirgin yawon wadanda ke da rajista da Hukumar ta NAHCON