Daga: Ibrahim Abubakar Nagarta-NHMST
A baya-bayan nan ne kungiyar ‘yan jaridu dake tallafawa harkokin aikin Haji ta Najeriya ta sake cin karo da wani rade-radin rashin daidaito, son zuciya da kuma rahoton da ba ayi bincike a kan ba a kafafen yada labarai na wata jarida ta yanar gizo mai suna “Daily Nigerian” tana zargin shugabancin NAHCON da nuna son kai.
Idan dai za a iya tunawa, kusan watanni 2 da suka gabata, wani rahoto makamancin haka wanda ya kasance mai alaka da na baya-bayan nan, wani dandali na kafafen yada labarai na daban ya yada wa al’umma ba tare da sanin ya kamata ba, abin da ya banbanta shi ne cewa rahoton na baya-bayan nan an alakanta shi ne ga kungiyar manyan ma’aikatan gwamnati ta Najeriya, na NAHCON, duk da cewa kungiyar ta nesanta kanta da rahoton, duk da haka, rahotannin biyu sun ta’allaka ne kan manufa guda daya da suka hada da batanci da bata sunan shugabancin hukumar ta NAHCON a halin yanzu ta hanyar lakabi zarge-zarge marasa tushe na son zuciya, son zuciya da gazawa, a kan shugaban NAHCON Farfesa Abdullahi Sale Usman wanda ya jagoranci kawo gyara a harkokin aikin haji a idon musulmin Najeriya wanda tun tsawon shekaru ake ta neman samun irin wannan ci gaba.
Duk da haka jaridun guda biyu sun yi ikirarin cewa sun samo bayanan marasa tushe daga cikin hukumar musamman na baya-bayan nan, amma abin takaici masu bayar da wadannan rahotannin da ke cike da cece-kuce ba su taba yin amfani da salon jin ta daya bangaren ba a matsayin muhimman ka’ida na aikin jarida ba kamar yadda ka’idojin aikin suka bukata kafin su yi gaggawar sakin labarin.
Wannan dabi’a ta yi nuni da yadda suka yi aiki nesa-nesa da bin ka’idodi da doka da ake bi wajen gudanar da aikin jarida a matsayin wani fanni na kwararru.
Sai dai abin takaici, ko kuma aka yi sa’a, rahoton da kafafen yada labarai na baya-bayan nan da suka fitar ya zo ne a daidai lokacin da dimbin musulmin Najeriya masu kishin kasa ke bayyana farin ciki, da kwarin guiwa da kuma amincewa da salon jagorancin shugaban hukumar alhazai ta kasa, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ganin irin nasarorin da ba a taba samu ba a cikin kankanin lokaci na shugabancin hukumar.
Babban abin da ya fi daukar hankalin na nasarorin Farfesa Abdullahi Saleh Usman, shi ne irin tsauraran matakan da shugaban mai hangen nesa da tawagar ma’aikatansa masu himma suka dauka wajen kula da kudin aikin hajjin 2025, daga sama da abin da aka biya a shekarar da ta gabata, duk da sauyin da ake samu a kasuwar hada hadar kudaden kasashen waje, hakan ya samu ne ta hanyar hadin kai da shawarwari tare da masu ruwa da tsaki na hukumar ta NAHCON.
Gaskiya-Bincike Game da Sanya ‘yan Uwa Cikin Aiki:
Da farko dai rahoton da jaridara ‘Daily Nigeria’ suka fitar kwanan nan ba su da sahihanci da ma’auni gaba daya, musamman inda ta bayyana sunan wani Abdulmalik Diggi, a matsayin dan uwan shugaban NAHCON, kamar yadda binciken NHMST, ya nuna, Diggi ba ya da alaka ta jini da shugaban, sai dai kawai makusancinsa da amintacce ne na shugaban da Farfesa Abdullahi Saleh zai iya ba shi mukamin, wanda hakan ke nufin ya nada shi domin ya taimaka masa wajen samun nasarar aikin Haji
Hakazalika, inda jaridar “Daily Nigerian” ta yanar gizo ta sake ba da labarin cewa, ta tattaro wasu bayanai daga cikin hukumar kamar yadda ta saba cewa wai ana shirin kwashe ma’aikatan hukumar zuwa wasu ma’aikatu inda gungun ma’aikatan NAHCON zai shafa, duk da cewa jaridar ta kasa bayar da wata kwakkwarar hujjar da za ta iya tabbatar da hakan, amma kamar yadda ta saba ta yi amfani da wata Kalmar cewa daga cikin Hukumar a matsayin tushen labarinta
An san ’yan jarida a ko da yaushe da rashin tsoro da jajircewa kamar haka, marubucin wannan labarin kanzon kurege kuma mai cike da rudani, ya kamata ace ya bugi kirgi ya bayyana sunan su wadanda sika bas hi labarin da zummar sun nemi a sakaya sunayensu
A shawarce wannan tunani zai karawa jaridar samun Karin kwarin gwiwa da amincin jama’a wanda shine babban fatan kowace kafar labarai mai inganci.
A karshe, babbar tambayar da ‘yan Najeriya da dama ke yi a yanzu ita ce, shin a gaskiya wa ke da hannu a cikin rahoton da jaridar “Daily Nigerian” ta buga mai cike da rudani, tun bayan da kungiyar manyan ma’aikatan Najeriya na NAHCON ta musanta fitar da wani rahoto na wannan dabi’a kamar yadda ake danganta ta da shi? a yayin da ire-iren wadannan rahotanni marasa tushe ke ci gaba da fitowa a kafafen yada labarai ba tare da tuntubar wadanda ake zargi ba (na bangare na uku) ba kamar yadda ka’idojin aikin jarida suka bayyana, kungiyar ta Nigerian Hajj Media Support Team (NHMST), za ta kasance ba ta da wani zabi da ya wuce ta fara kama suna, ta hanyar fallasa wadanda suka dauki nauyin wadanda ake zargi da yin kiraye-kirayen domin jama’a su sansu, ba tare da la’akari da wadanda ba su da alaka da rubutaccen suna. don bata sunan Farfesa Abdullahi Saleh Usman, suna cikin ko wajen aikin hajji ko kuma musamman hukumar alhazai ta kasa.