Shugaban Ƙasa ya umarci Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) da ta fitar da sabon farashi cikin kwanaki biyu.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ne ya isar da umarnin Shugaban Ƙasa yayin wani taro da ya gudana da shugabannin hukumar NAHCON a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, a ranar Litinin.
Ya bukaci a samu haɗin kai tsakanin jami’an ƙasa da na jihohi, ciki har da gwamnonin jihohi, wajen tsara da kuma amincewa da sabon tsarin farashin aikin Hajjin.
Haka kuma, ya jaddada bukatar daukar matakin gaggawa daga dukkan masu ruwa da tsaki don tabbatar da biyan kuɗaɗe cikin lokaci da aika su zuwa Babban Bankin Najeriya (CBN), domin gudanar da aikin Hajji ba tare da tangarda ba.
Yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai bayan kammala taron da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Mataimakin Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia, ya bayyana cewa taron ya gudana ne domin kammala shirye-shiryen aikin Hajjin 2026, musamman wajen tantance farashin aikin.
Ya bayyana cewa manufar gwamnati ita ce rage nauyin kuɗin da maniyyata za su biya, duba da halin tattalin arzikin ƙasa da sauye-sauyen da ake aiwatarwa a wannan lokaci.
Ya ce, “Farashin musayar kuɗi na ƙasa da ƙasa yana ci gaba da ingantuwa, kuma darajar naira tana ƙaruwa sakamakon gyare-gyaren tattalin arzikin da gwamnati ke aiwatarwa. Mataimakin Shugaban Ƙasa ya lura cewa idan maniyyata sun biya tsakanin Naira miliyan 8.5 zuwa 8.6 bisa ga tsohon farashin musayar kuɗi, yanzu da naira ta ƙara ƙarfi, to ya dace a rage kuɗin aikin, domin maniyyata su amfana da sauyin.”
“Don haka, hukumar NAHCON da jami’anta sun samu umarni da su koma su sake nazari bisa sabon farashin musayar kuɗi. Idan muka cimma abin da muke fata, za a samu gagarumin sauƙin kuɗin aikin Hajji.”
A nasa bangaren, Sakataren Hukumar Alhazai ta Ƙasa, Dokta Mustapha Muhammad, ya bayyana cewa umarnin Shugaban Ƙasa zai ƙara yawan maniyyatan da za su yi aikin Hajji a bana.
“Wannan ci gaba ne mai kyau, domin idan an rage kuɗin aikin Hajji, zai fi sauƙi ga musulmai da dama da ke da niyyar zuwa. Saboda haka, kamar yadda Mataimakin Shugaban Ƙasa ya umurce mu, za mu yi aiki tukuru daga yau zuwa gobe don ganin mun rage farashin zuwa mafi ƙaranci, domin kowa da kowa ya samu damar aiwatar da wannan muhimmin rukuni na addinin Musulunci.”
Haka kuma, Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kebbi, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar Shugabannin Hukumar Alhazai na Jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Alhaji Faruk Aliyu Yaro, ya nuna farin ciki da wannan umarni daga shugaban ƙasa.
Ya ce, “Muna matuƙar farin ciki saboda Shugaban Ƙasa da Mataimakin Shugaban Ƙasa sun riga sun shiga tsakani. Muna gode wa Allah bisa wannan mataki, wanda ake sa ran zai rage farashin aikin Hajji. Don haka muna farin ciki ƙwarai.”
(Daily Trust)