Daga: Ibrahim Abubakar, Nagarta
Kungiyar Ƙwararrun ‘Yan Jaridu Ɗaukar Rahotannin Harkokin Hajji (AHMSP), ƙungiya ce ta farar hula da ke bibiyar abubuwan da ke faruwa a cikin harkokin aikin hajji na Najeriya, tana bayyana cikakken goyon bayanta da na ƙwarin gwiwa ga kiran da wasu ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da ƙungiyoyi kamar Independent Hajj Reporters (IHR) da Association of Hajj Media Support Professionals (AHMSP) suka yi ko dai a matsayin maimaita kiran da shugaban hukumar NAHCON mai ci, Farfesa Abdullahi Saleh Usman (Pakistan), ya riga ya yi tun bayan da aka naɗa shi a matsayin shugaban hukumar aikin hajji ta kasa, a ranar 19 ga Agusta, 2024, daga shugaban ƙasa Mai Girma Bola Ahmed Tinubu.
Sabbin kiraye-kirayen da wasu ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa suka yi akan wannan batu suna zama hujja ta gaskiya cewa manufar shugaban hukumar na alheri ce ga mahajjatan Najeriya.
A gaskiya, ya kamata a taya Farfesa Saleh murna, wanda shi ne ya fara wannan kira mai muhimmanci ga Babban Bankin Najeriya (CBN), da a daina cire harajin kashi 2% da ake karɓa daga mahajjatan Najeriya shekaru da dama kenan.
Shugaban NAHCON ya gudanar da taruka da dama da manyan jami’an Babban Bankin Najeriya tare da neman taimakon wasu fitattun ‘yan Najeriya domin a samu nasarar wannan muhimmiyar bukata.
Ya himmatu yana kokari wajen inganta harkar gudanar da aikin hajji a Najeriya, duk da cewa wasu masu son kai da adawa suna ci gaba da yada zarge-zarge marasa tushe kan mutuncinsa da aikinsa!
Sai dai har yanzu fafutukar ba ta ƙare ba, domin Babban Bankin Najeriya bai amince da wannan roƙo na soke harajin kashi 2% ba. Saboda haka, lokaci ne da dukkan masu ruwa da tsaki su haɗa kai domin marawa Farfesa Abdullahi Saleh Usman baya a wannan kyakkyawar manufa har sai an cimma nasara.
Ya kamata a tuna cewa, mahajjatan Najeriya na yin addu’a mai ƙarfi don samun haɗin kai da ci gaban tattalin arzikin ƙasa yayin da suke a ƙasar mai tsarki. Wannan ne ya sa daina cire harajin kashi 2% daga gare su zai zama wata babbar gudunmawa ta ƙasa, fiye da kowanne abu na amfani.
Lallai shugaban NAHCON da kwamishinoni da sauran ma’aikatansa suna taka rawar gani wajen biyan bukatun al’ummar Najeriya, musamman musulmai, ganin irin ragin kudaden da aka samu ga mahajjatan 2026 daga masu yi wa Alhazai hidima a Saudiyya kamar masauki, abinci, sufuri, da ayyukan Mashaa’ir wanda ya kai sama da naira biliyan 19, sakamakon tattaunawarsu ta kwanan nan a ƙasar Saudiyya.
Wannan nasara tana daidaita da manufar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Haka kuma, Independent Hajj Reporters suna da cancantar yabo saboda goyon bayansu ga wannan kira na gaskiya da zai kawo sauƙi ga mahajjata da al’ummar musulmi baki ɗaya, tare da fatan wannan kishin ƙasa da suka nuna zai ci gaba da dorewa.
A ƙarshe, ƙungiyar Association of Hajj Media Support Professionals (AHMSP) tana mika goyon bayanta na gaskiya da fatan alheri ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, bisa amincewa da jajircewar Farfesa Abdullahi Saleh Usman wajen jagorantar Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) cikin gaskiya da nagarta.