Kwamitin majalisar wakilai mai kula da aikin hajji ya sha alwashin bincikar yadda kowane mahajjatan Najeriya 95,000 suka biya Naira miliyan 8.1 a matsayin kudin aikin Hajjin shekarar 2024.
Da yake zantawa da Muryar Amurka, shugaban kwamitin, Ja’afaru Damisa, ya ce majalisar za ta binciki nawa aka kashe a kan kowane mahajjaci a dukkan bangarorin aikin Hajji.
Mista Damisa, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Borgu da Agwara, ya ce kwamitin ya yanke shawarar kaddamar da binciken ne duba da yadda ake ta yada jita-jitar cewa aikin Hajjin 2025 zai kai Naira miliyan 10 ko fiye.
Ya ce kwamitin zai gayyaci jami’an hukumar alhazai ta kasa NAHCON domin yin bayani kan kudaden da aka kashe na kowane mahajjaci da nawa ya rage.
Shettiman Barkum ya ce nan ba da dadewa ba za a gudanar da a shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin 2025.
“Za mu binciki yadda mahajjatan Najeriya suka biya Naira miliyan 8.1 kudin aikin Hajjin 2024.
“Wannan ya biyo bayan rade-radin da ake ta yadawa cewa aikin Hajji mai zuwa zai kai Naira miliyan 10 ko ma sama da haka.
“Za mu gayyato jami’an da su yi mana bayanin nawa aka kashe a kan wuraren kwana na jirgin sama, ciyar da abinci da sauran abubuwan da aka kashe sannan mu ga nawa aka kashe da nawa ya rage.
“Idan akwai wasu kudade da suka rage, za mu tabbatar da mayar da kudaden ga maniyyata cikin gaggawa, domin shirye-shiryen aikin Hajjin 2025,” kamar yadda ya shaida wa Muryar Amurka a cikin shirinta na mako-mako, “Manuniya”
Shugaban kwamitin ya kuma bayyana kwarin guiwar sabon shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Abdallah Saleh-Usman da ya kai hukumar alhazan ga nasara
A cewar Mista Damisa, “muna da kwarin guiwa a gare shi bisa la’akari da dimbin ilimin da yake da shi na addinin Musulunci da kuma shekarun da ya yi a aikin Hajji.
“Muna da kwarin gwiwa a gare shi kuma za mu ba shi cikakken hadin kai don kai Hukumar ga burin da aka sanya a gaba ,” in ji shi.
(Daily Nigeria)