Daga Muhammad Ahmad Musa
Ministan lafiya na Najeriya, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya kammala wata gagarumar ziyarar aiki zuwa cibiyoyin kula da lafiya na hukumar kula da aikin Hajji ta kasa (NAHCON) a birnin Makkah na kasar Saudiyya, lamarin da ke nuna cewa an samu sauyi a kokarin gwamnatin tarayya na bunkasa harkokin kiwon lafiyar alhazai.
A ziyarar da ya kai ofishin hukumar NAHCON ta Ummul-Jud, Minista Pate ya ba da tabbacin goyon bayan gwamnati da nufin tunkarar kalubalen kiwon lafiya da alhazan Najeriya ke fuskanta yayin aikin Haji.
A Sanarwar da shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar, Muhammad Ahmad Musa ya sanyawa hannu, yayin ziyarar ofishin hukumar dake Ummul Jud ,ta nuna wani kuduri mai zurfi na gwamnatin tarayya, wanda ke nuna bayar da fifikon jin dadin alhazai da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi.
“Aniyarmu a bayyane yake,” in ji Minista Pate yayin tattaunawa da jami’an NAHCON.
“Idan aka yi la’akari da yanayin kiwon lafiya a duniya tun daga barkewar cutar sankarau da cutar shan inna, ya zama wajibi mu cika kuma mu wuce ka’idojin kiwon lafiya na Saudiyya. Tabbatar da sahihan takardun rigakafin, gami da katin gargadi ga dukkan mahajjatan Najeriya,wani abu ne da ya zama wajibi
Ministan Pate wanda ya samu rakiyar manyan wakilan ma’aikatar lafiya, ya gudanar da cikakken aikin duba motocin daukar marasa lafiya na NAHCON, da duba kayyakin da magunguna, da kuma tantance shirye-shiryen kayan aiki a asibitocin Najeriya da ke kasar Saudiyya.
Ziyarar ta bayyana wasu muhimman bangarori da ake bukatar ingantawa, da suka haɗa da haɓaka samar da muhimman magunguna, alluran rigakafi, na’urorin likitanci, da motocin daukar marasa lafiya masu aiki.
Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yabawa shirin na Ministan, inda ya jaddada muhimmancinsa: “shigowarka cikin wannan tsari yayi nuni da yadda ake shirin sake inganta aikin kula da lafiyar alhazai Ganin yadda ‘yan Najeriya kusan 70,000 ke halarta a duk shekara, ziyarar aikin da Ministan Pate ya yi ya nuna wani muhimmin ci gaba a cikin sa ido na gwamnati da tsare-tsare na kiwon lafiya.
Ya kuma yi tsokaci kan matsalolin da suka kunno kai, musamman yanayin zafi mai yawa a lokacin aikin Hajjin 2025 mai zuwa, tare da daukar matakan da suka dace don kiyaye lafiyar alhazai da walwala.
Wannan gagarumar ziyarar aiki i ta samar da ingantaccen hadin gwiwa tsakanin ma’aikatar lafiya ta Najeriya da NAHCON, tare da tabbatar da cewa mahajjatan Najeriya sun samu kulawa ta musamman a lokacin tafiyarsu ta Ibada
Hukumar NAHCON ta nanata sadaukarwar ta ga gaskiya, ba da hidima ta musamman da kuma ci gaba da inganta jin dadin alhazai.
Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Mohammed Ali Pate ne ya gudanar da ziyarar, tare da rakiyar Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, Kwamishinan Ayyuka, PRSILS da PPMF, Prince Anofi’u Olanrewaju Elegusi, Farfesa Abubakar AbubakarYagawal; Prince Abdul-Razaq Aliyu, da kuma mamba mai wakiltar ma’aikatar lafiya ta tarayya Dr.Sa’edu Ahmad Dumbulwa.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Sakataren Hukumar Dokta Muhammad Mustapha Ali, Daraktoci, Mataimakan Daraktoci, da mataimakin Jami’in Hulda da Jama’a na Saudiyya Abubakar Lamin da sauran ma’aikatan Hukumar.